Tsohon gwamnan Jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi kira ga magoya bayansa da daukacin ‘yan Najeriya da su shiga jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC) bayan sauya shekarsa zuwa jam’iyyar.
Kwankwaso ya bayyana hakan ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na X ranar Litinin, inda ya ce matakin ya samo asali ne daga kishin dimokuraɗiyya da kuma bukatar samar da sahihiyar jam’iyyar siyasa.
“Jiya mun dauki babban mataki mai muhimmanci ta hanyar shiga jam’iyyar Nigeria Democratic Congress a hukumance,” in ji Kwankwaso.
Ya kara da cewa:
“Mun kuduri aniyar samar wa al’ummarmu ingantacciyar jam’iyya da za ta bai wa jama’a damar ci gaba da cimma burinsu.”
Tsohon ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP ya bukaci ‘yan Najeriya su mara wa NDC baya domin tabbatar da shugabanci nagari da cikakkiyar dimokuraɗiyya.
“Ina kira ga dukkan magoya bayanmu da masu kishin kasa su shiga NDC domin ci gaba da wannan gwagwarmayar samar da shugabanci nagari,” ya bayyana.
Rahotanni sun nuna cewa Kwankwaso da Peter Obi sun shiga NDC ne a hukumance a wani taro da aka gudanar a Abuja, yayin da ake ci gaba da sauye-sauyen siyasa gabanin babban zaben shekarar 2027.
A nasa jawabin, Peter Obi ya bayyana cewa sun yanke shawarar shiga NDC ne domin samun jam’iyya mai zaman lafiya ba tare da rikice-rikicen cikin gida ba.
Kwankwaso ya kuma ce tattaunawarsu da shugabannin NDC ta nuna cikakkiyar daidaito a manufofi, musamman ta fuskar:
Ilimi
Karfafa matasa
Tsaro
Hadin kan kasa
Ya kuma gayyaci ‘yan Najeriya ciki har da mazauna kasashen waje masu sha’awar shiga siyasa da su yi rajista da jam’iyyar cikin gaggawa.
Masana siyasa na ganin wannan sauya sheka ta Kwankwaso da Obi zuwa NDC na iya sauya yanayin siyasar Najeriya yayin da ake tunkarar zaben 2027
