Gwamnan Jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya ƙaryata rahoton da ke cewa tsohon gwamna, Sanata Umaru Tanko Al-Makura, ne ya kawo shi kan mulki a 2019, inda ya ce duk da goyon bayan da Al-Makura ya ba shi, ba shi kaɗai ne ya sanya shi ya zama gwamna ba.
Da yake magana a shirin Sunday Politics na Channels Television, Gwamna Sule ya ce nasararsa ta samo asali ne daga cancantarsa ta aiki, ba wai wani ya “ɗauko shi daga ko’ina ba”.
Ya ce: “Ba shi ne ya kawo ni ofis ba; ya goyi bayana ne lokacin da nake neman ofis. Bai ɗauko ni daga ƙasa ba; ya san ni a matsayin babban darakta janar na kamfani mai rajista.”
Gwamnan ya kuma musanta batun cewa Al-Makura shi ne ubangidansa na siyasa, inda ya bayyana shi a matsayin malami ko mai horas da shi a siyasa.
“Ba ubangidana ba ne; ya koya mini siyasa,” in ji shi.
Wannan batu na zuwa ne a daidai lokacin da ake rahoton sabani tsakanin su biyu kan batun wanda zai gaji mulki a 2027 a Jihar Nasarawa.
Sule ya ce kowa na da ‘yancin goyon bayan duk wani ɗan takara da yake so, amma ba wanda ke da ikon tilasta masa ya karɓi wani zaɓi.
Ya kuma yi zargin cewa ana gudanar da tarukan wani ɗan takara a gidan Al-Makura, kuma wasu daga cikin mukarrabansa ma ana ƙoƙarin shigar da su cikin wannan tafiya.
“Ba wani sirri ba ne cewa kusan duk tarukan wannan ɗan takara ana yi a gidansa. Har ma ya gayyato wasu daga cikin mukarrabana ya ce su mara masa baya,” in ji Sule.
Gwamnan ya bayyana cewa matsayinsa ya samo asali ne daga ra’ayin adalci na rabon mulki (zoning), inda ya ce bai dace a mayar da mulki yankin da ya rike shi tsawon shekaru 12 ba.
“Ina ganin ba adalci ba ne a koma yankin da ya rike mulki tsawon shekaru 12. Wannan shi ne dalilina,” ya bayyana.
Duk da sabanin ra’ayi, Gwamna Sule ya jaddada cewa yana da kyakkyawar dangantaka da Al-Makura, kuma yana girmama shi.
Ya ce: “Na nuna masa godiya a ko’ina… amma goyon baya ba yana nufin dole ne ka mallaki duk shawarar wanda ka goyi baya ba.”
Ya kara da cewa kowa na da ‘yancin zabar wanda yake so, amma ba wanda zai tilasta masa ya karɓi ra’ayin da bai yarda da shi ba.
“Zan zaɓi wanda zai gaje ni, kuma wannan ba wuce gona da iri ba ne,” in ji shi.
A baya-bayan nan dai Gwamna Sule ya bayyana Sanata Aliyu Ahmed Wadada a matsayin wanda yake goyon baya domin tikitin jam’iyyar APC a zaben gwamna na 2027 a Nasarawa.
