Tsohon ɗan Majalisar Wakilai kuma jigo a jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Gbenga Makanjuola, ya karɓi fom ɗin takarar jam’iyyar domin neman kujerar Sanatan Kwara Kudu gabanin babban zaɓen shekarar 2027.
Makanjuola ya bayyana aniyarsa ne yayin wata ziyara da ya kai hedikwatar APC ta Jihar Kwara da ke Ilorin a ranar Juma’a, inda ya gana da mambobin kwamitin zartarwa na jihar ƙarƙashin jagorancin shugaban jam’iyyar, Sunday Fagbemi, sannan ya miƙa wasikar aniyarsa a hukumance.
Ya ce: “Na zo ne da yardar Allah domin nuna sha’awata ta wakiltar Kwara Kudu a sabuwar wa’adin mulki. Duk abin da mutum ya faɗa ko ya yi, Allah ne ke bayar da nasara.”
Tsohon ɗan majalisar ya ce shawarar sake shiga takara ta samo asali ne daga ƙudirinsa na ci gaba da hidimar jama’a, yana mai tunatar da cewa nasarorin da ya samu a baya sun dogara ne kan aiki tuƙuru da goyon bayan jama’a ba tare da sayen kuri’u ba.
Ya ce: “A zaɓen da na yi a baya, babu wani wakili da ya karɓi ko sisin kwabo daga gare ni, ko a matakin fidda gwani ko babban zaɓe. Wannan shaida ce ta ni’imar Allah da kuma amincewar jama’a.”
Makanjuola ya bayyana cewa ya yi shekaru kusan 16 a tsarin Majalisar Dokoki ta Ƙasa, ciki har da lokacin da ya yi a matsayin ɗan majalisa, Mataimakin Shugaban Ma’aikata ga Shugaban Ƙasa, da kuma sauran ayyukan da ya yi tare da shugabancin Majalisar Dattawa.
Ya ƙara da cewa manufar wakilci ita ce kasancewa kusa da jama’a da kare muradunsu, yana mai cewa zai riƙe gaskiya da tsoron Allah idan aka ba shi dama.
Ya kuma tuna cewa bayan kammala wa’adinsa, ya ziyarci dukkan ƙananan hukumomi 42 na mazabarsa domin gode wa jama’a, yana mai cewa hakan ya nuna gaskiya da kusancinsa da al’umma.
A nasa ɓangaren, Shugaban APC na Jihar Kwara, Sunday Fagbemi, ya bayyana Makanjuola a matsayin mutum mai kamun kai da nagarta.
Ya ce: “Mutum ne nagari, mai tawali’u da gaskiya. Idan a ce ina da ikon ba shi tikiti nan take zan yi hakan. Amma kamar yadda muka sani, Allah ne ke ƙarshe yake bayar da mulki.”
