Wata ƙungiyar siyasa mai zaman kanta, Public Enlightenment Movement (PEM), ta bayyana cewa Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu na da cikakken niyyar gina Najeriya mai ƙarfi, haɗaɗɗiya da kuma mai haɗin kai ta hanyar ci gaban ababen more rayuwa da shirye-shiryen jin daɗin jama’a a faɗin ƙasar.
Ko-odinetan ƙasa na ƙungiyar, Nuhu Abdullahi, ne ya bayyana hakan a Kano yayin gabatar da kashi na bakwai na rahoton ayyukan PEM kan muhimman ci gaba da aka samu a Arewacin Najeriya a ƙarƙashin wannan gwamnati.
Ya ce an tsara shirin ne domin bayar da sahihan bayanai kan ayyukan gwamnati tare da ƙarfafa gaskiya da bayyana gaskiya, inda ya ce wannan sabon kashi ya nuna gagarumin ci gaba a fannin hanyoyi da ke inganta haɗin yankuna.
Ya misalta aikin gyaran hanyar Ajingi–Jahun–Kafin Hausa da ke haɗa Jihar Kano da Jigawa, inda ya ce hakan zai taimaka wajen sauƙaƙa jigilar amfanin gona da ƙarfafa harkokin tattalin arziki.
A cewarsa, aikin mayar da hanyar Minna–Bida mai layi biyu a Jihar Neja zai rage lokacin tafiya tare da ƙara tsaro, yayin da aikin Kaduna Western Bypass zai rage cunkoso da inganta shiga babban birnin tarayya Abuja.
Haka kuma, ya ce gyaran hanyar Shiroro a Jihar Neja ya taimaka wajen inganta haɗin kai da dawo da harkokin tattalin arziki a yankin.
A bangaren lafiya, Abdullahi ya ce kafa cibiyar cutar daji (cancer) a Asibitin Koyarwa na Tarayya da ke Katsina babban ci gaba ne wajen samar da ingantaccen kulawar lafiya mai sauƙi ga jama’a.
Ya kuma bayyana cewa ana ci gaba da aikin babban titin Sokoto–Badagry Superhighway, wanda ya ce zai zama babbar hanyar haɗa jihohi da dama domin bunƙasa kasuwanci da sauƙaƙa zirga-zirga tare da tanadin tsaron zamani.
Ya ce waɗannan ayyuka suna nuna manufofin shirin Renewed Hope na gwamnati, yana mai cewa ci gaban da ake samu a Arewa yana nuna ƙoƙarin da ake yi wajen haɓaka ƙasa baki ɗaya.
A ƙarshe, ya tabbatar da cewa ƙungiyarsu za ta ci gaba da wayar da kan jama’a kan ayyukan gwamnati, yana mai cewa dorewar wayar da kai na da matuƙar muhimmanci wajen ci gaban ƙasa.
