Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa National Bureau of Statistics (NBS) ta bayyana cewa farashin litar fetur a Najeriya ya ƙaru daga N1,051.47 a watan Fabrairu zuwa N1,288.54 a watan Maris na 2026.
A cikin rahotonta mai taken Premium Motor Spirit (Petrol) Price Watch da aka fitar a Abuja, NBS ta ce wannan ƙaruwa tana nufin hauhawar kashi 22.55% a tsakanin watanni biyu.
Rahoton ya kuma nuna cewa idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata, farashin ya ƙaru da kashi 2.13%.
Jihohi da yankuna
Rahoton ya nuna cewa jihar Anambra ce ke da mafi tsadar fetur da N1,441.22 a kowace lita, sai Sokoto da N1,377.55, da Borno da N1,375.16.
A gefe guda, Lagos ta fi sauƙin farashi da N1,162.71, sai Ogun da Kaduna.
A bangaren yankuna, Arewa maso Gabas ce ke da mafi tsadar fetur, yayin da Kudu maso Yamma ke da mafi arha.
Farashin dizal ma ya ƙaru
Rahoton ya ƙara da cewa farashin dizal ya tashi da kashi 16.05% daga N1,420.17 a Fabrairu zuwa N1,648.08 a Maris.
Ebonyi ce ke da mafi tsadar dizal da N2,262.29, sai Akwa Ibom da Osun. Jihar Kogi kuma ce ke da mafi arha.
Dalilin tashin farashi
Masana tattalin arziki sun danganta wannan hauhawar farashi da rikice-rikicen siyasa a Gabas ta Tsakiya da suka shafi samar da man fetur a duniya.
Wani masanin tattalin arziki, Opeyemi Alabi, ya ce rikicin Amurka da Iran ya kawo cikas ga hanyoyin samar da mai, wanda ya haifar da hauhawar farashin man fetur a duniya.
Ya ce: “Farashin fetur yanzu ya kai N1,600 a wasu wurare, yayin da dizal ya wuce N2,000. Wannan yana ƙara tsadar sufuri da rayuwa a Najeriya.”
Idan wannan yanayi ya ci gaba, masana sun yi gargadin cewa zai iya ƙara tayar da hauhawar farashin kayayyaki a ƙasar.
