Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ta zargi jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki da haddasa rikice-rikice a cikin jam’iyyun adawa, musamman jam’iyyar Peoples Redemption Party (PRP), tana mai gargadin cewa hakan na iya barazana ga zaman lafiyar dimokuradiyyar Najeriya.
A cikin wata sanarwa da Kakakin Yada Labarai na ADC na kasa, Bolaji Abdullahi, ya wallafa a shafinsa na X, ya yi kakkausar suka ga gwamnati yana cewa: “Wannan shi ne gwamnati mafi rashin kunya a tarihin Najeriya.”
Abdullahi ya ce ‘yan kwanaki bayan wata ziyara da shugabancin PRP ya kai ga shugaban ADC, jita-jita ta fara yawo kan yiwuwar kawance tsakanin jam’iyyun.
Ya bayyana cewa wannan jita-jita ce ta haifar da bullowar wani bangare a cikin PRP cikin gaggawa, wanda ya fara kalubalantar shugabancin Hakeem Baba-Ahmed.
A cewarsa, wannan lamari yana nuna irin matsin da dimokuradiyya ke fuskanta a karkashin mulkin APC, yana mai cewa akwai alamar cewa ana kokarin raunana jam’iyyun adawa.
Ya kara da cewa duniya na lura da abin da ke faruwa, kuma hakan na iya kaiwa ga rikitar da tsarin siyasar kasar nan idan ba a dauki mataki ba.
Abdullahi ya kuma yi tambaya ko babu masu hankali a cikin APC da za su gargadi irin wannan dabi’a, yana mai cewa hakan na iya zama barazana ga zaman lafiya na kasa.
A karshe, ya ce duk wani yunkuri na lalata jam’iyyun adawa zai iya cutar da tsarin dimokuradiyya, domin idan aka bar jama’a babu zabi a siyasa, hakan na iya jefa kasa cikin matsala.
