Magoya bayan tsohon Gwamnan Jihar Anambra, Peter Obi, da kuma tsohon Gwamnan Jihar Kano, Rabiu Kwankwaso, sun ƙaddamar da sabuwar ƙungiyar matsin lamba ta siyasa mai suna Obi–Kwankwaso (OK) Movement, a daidai lokacin da ake ƙara samun sauye-sauyen haɗin kai a fagen siyasar Najeriya gabanin zaben fidda gwani na shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam’iyyar ADC domin zaben 2027.
Ƙungiyar ta bayyana kafuwarta ne a Abuja a ranar Litinin, inda ta ce ta riga ta kafa tsarin aiki a dukkan jihohi 36 na ƙasar da kuma Babban Birnin Tarayya (FCT), tare da nada shugabanni a matakin jihohi da shiyya domin jagorantar wayar da kai da tura saƙon siyasa.
Sakataren Yada Labarai na ƙungiyar na ƙasa, Justin Ijeh, ya bayyana hakan a wata sanarwa, inda ya ce wannan shiri haɗin gwiwa ne na ƙungiyoyin siyasa da suka haɗa da Obidient Movement, Kwankwasiyya Movement, New Nigeria People’s Party (NNPP) da kuma ADC.
Wannan mataki na nuna sabon salo na haɗin kai a cikin kawancen ‘yan adawa, yayin da ake ci gaba da samun rudani kan wanda zai lashe tikitin shugaban ƙasa na ADC gabanin 2027.
OK Movement ya yi kama da tsarin Obidient Movement, wanda ya yi tasiri sosai a siyasar Najeriya a 2023 ta hanyar ƙarfafa matasa da jama’a a matakin ƙasa.
Ijeh ya ce Najeriya na cikin wani muhimmin lokaci mai cike da ƙalubale, inda ya ce ƙungiyar ta fito ne domin haɗa kai wajen neman sauyi da sake gina ƙasa.
Ya ce:
“Nijeriya na fuskantar matsin tattalin arziki, tsadar rayuwa da kuma matsalar tsaro. OK Movement na fitowa a matsayin fata ga al’umma.”
Ya ƙara da cewa ƙungiyar ba ta goyon bayan siyasar ƙabilanci ko addini, kuma tana neman haɗin kan ‘yan Najeriya gaba ɗaya.
Ya ce za a fara kaddamar da rassan ƙungiyar a jihohi nan ba da jimawa ba, tare da buɗe ƙofa ga duk wanda ke son sauyi a ƙasar.
A nasa bangaren, Shugaban Obidient Movement na ƙasa, Dr. Yunusa Tanko, ya tabbatar da cewa akwai haɗin kai tsakanin sabuwar ƙungiyar da sauran tsarin goyon bayan Obi, inda ya ce suna aiki tare domin burin samun tikitin shugaban ƙasa a ƙarƙashin ADC.
Ya ce: “Babu rabuwar kai. OK Movement da Village Boys Movement suna aiki ne domin manufa ɗaya.”
Wannan sabon yunƙuri ya biyo bayan ƙarin rikici a cikin ADC, musamman dangane da burin tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, wanda ya bayyana aniyarsa ta neman tikitin jam’iyyar.
Atiku ya ce ba zai janye wa wani ɗan takara ba, lamarin da ya jawo cece-kuce a cikin jam’iyyar.
Haka kuma, wasu jiga-jigan ‘yan siyasa kamar Rotimi Amaechi, Aminu Tambuwal da Nasir el-Rufai suna cikin waɗanda ake hasashen za su nemi tikitin ADC.
Jam’iyyar ADC, wacce tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, David Mark ke jagoranta, na ci gaba da jan hankalin manyan ‘yan siyasa a fadin ƙasar.
A gefe guda kuma, jam’iyyar Labour Party ta nesanta kanta daga wasu rubuce-rubuce a shafukan sada zumunta da ke kira ga Obi da Kwankwaso su koma jam’iyyar.
Shugabar riƙon jam’iyyar, Sanata Esther Nenadi Usman, ta ce waɗannan saƙonni ba su fito daga hedikwatar jam’iyyar ba.
Ta ce saƙonnin bogi ne kuma ba su wakiltar matsayar jam’iyyar Labour Party.
