Likitoci a Jihar Ondo sun ba gwamnati wa’adin kwana 8 ta biya musu alawus da inganta walwala.
Sun ce ba a aiwatar da wasu umarnin gwamnatin tarayya da suka shafi albashi ba, duk da cewa jihohi da dama sun riga sun fara.
NMA ta Ondo ta ce idan ba a biya bukatunsu cikin wa’adin ba, za su iya daukar matakin yajin aiki.
