Fitaccen mai sharhi da nazarin abinci a Najeriya, Opeyemi Famakin, ya bayyana cewa sha’awar mahaifiyarsa ga abinci ce ta kasance tushen tafiyarsa zuwa fagen nazarin abinci, ba wai don ya zama fitaccen mai tasiri a kafafen sada zumunta ba.
Famakin ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi a TJAE Podcast, wanda ɗan jarida Joey Akan ke gabatarwa.
Ya ce tun yana ƙarami ya taso ne a gidan da ake matuƙar son gwada nau’ikan abinci daga ƙasashe daban-daban.
A cewarsa, mahaifiyarsa da kakansa duk masu son abinci ne, kuma hakan ya sa iyalansu ke yin tafiye-tafiye zuwa ƙasashe daban-daban domin gwada nau’ikan abinci.
Ya bayyana cewa ya kai ziyara zuwa ƙasashe da dama, ciki har da Spain, Amurka, Birtaniya, Jamaica, Cayman Islands, Mexico, Bahamas da Dubai, inda ya ce daga cikin ‘ya’yan gidan, shi ne ya fi bin sahun mahaifiyarsa wajen sha’awar abinci.
Famakin ya ce bai taɓa tsara zama fitaccen mai ƙirƙirar abun ciki ko mai tasiri a shafukan sada zumunta ba.
Ya ce kawai yana son abinci ne kuma yana jin daɗin yin magana a kansa, kafin daga baya wannan sha’awa ta rikide zuwa sana’ar da ta sa ya shahara.
A cewarsa, “Ban taɓa yin wani babban shiri na zama fitacce ko mai tasiri ba. Ina son abinci ne kawai, ina kuma son tattaunawa a kansa. Daga baya abubuwa suka ci gaba da sauyawa har na zama abin da nake a yau.”
