Mashawarcin harkokin gudanarwa da dabarun ƙungiyoyi, Michael Ugbewanko, ya samu shiga cikin Forbes Human Resources Council, wata ƙungiya ta musamman da ke haɗa manyan ƙwararru a fannin kula da ma’aikata, shugabannin kamfanoni da masu ruwa da tsaki a harkokin kasuwanci daga sassa daban-daban na duniya.
Ugbewanko, wanda shi ne babban mashawarci a kamfanin Dmidaf Global Consult, ya shiga jerin fitattun ƙwararrun da ke ba da gudunmawa wajen inganta shugabanci, gudanar da ƙungiyoyi da bunƙasa albarkatun ɗan Adam a matakin duniya.
A cewar wata sanarwa, membobin Forbes Human Resources Council na samun damar rubuta maƙalu a shafin Forbes, yin haɗin gwiwa da sauran ƙwararru, da kuma cin gajiyar shirye-shiryen bunƙasa ƙwarewa.
Da yake magana kan wannan nasara, Ugbewanko ya ce samun damar shiga ƙungiyar wata babbar dama ce ta bayyana ra’ayoyin Afirka a tattaunawar duniya kan shugabanci da ci gaban ƙungiyoyi.
Ya ce ƙungiyoyin da ke gina ingantattun tsare-tsare tare da bai wa ma’aikata damar yin aiki yadda ya kamata su ne za su jagoranci harkokin kasuwanci a nan gaba.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa Ugbewanko ya shafe fiye da shekaru goma yana ba shugabannin kamfanoni shawara kan tsarin gudanarwa, shugabanci da kula da albarkatun ɗan Adam.
A shekarar 2025, mujallar Entrepreneur Magazine ta saka shi cikin jerin manyan shugabannin HR guda 10 mafi tasiri a Afirka. Haka kuma shi ne marubucin littafin “HR Is Dead”, wanda ya yi bayani kan yadda aikin kula da ma’aikata ke sauyawa domin inganta ayyukan ƙungiyoyi.
Baya ga aikin ba da shawara, Ugbewanko yana jagorantar Operational Excellence Conclave da kuma The Presidential Table, dandamali da ke haɗa manyan shugabannin kamfanoni da jami’an gwamnati domin musayar dabaru kan shugabanci.
Ya samu digirin digirgir na biyu (Master’s) a fannin Human Resource Management daga Jami’ar South Wales ta Birtaniya, sannan yana da digiri a fannin Falsafa daga Jami’ar Ibadan.
