Fadar Shugaban Ƙasa ta bayyana cewa yabon da Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu wata ƙarin shaida ce da ke nuna irin ci gaban da gwamnatin ke samu wajen yaƙi da ta’addanci da inganta tsaro a Najeriya.
Mai ba Shugaban Ƙasa shawara kan harkokin sadarwa da manufofi, Daniel Bwala, ne ya bayyana hakan yayin wata hira da ya yi a shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels TV.
Bwala ya ce wasiƙar yabon da Trump ya aike wa Shugaba Tinubu ta nuna cewa ƙasashen duniya na ganin irin ƙoƙarin da gwamnatin Najeriya ke yi wajen magance matsalolin tsaro.
Ya ce, “Gaskiya tana magana da kanta. Wannan wasiƙa wata ƙarin shaida ce ta ci gaban da muke samu.”
Trump, a cikin wasiƙarsa mai ɗauke da kwanan watan 6 ga Yuli, 2026, ya yaba wa Tinubu kan jajircewarsa wajen yaƙi da ta’addanci da hare-haren da ake kai wa al’ummomi, tare da jaddada aniyar Amurka na ci gaba da tallafawa Najeriya a yaƙin da take yi da ta’addanci.
Sai dai Bwala ya jaddada cewa ko da ba a samu wannan yabo ba, gwamnatin Tinubu za ta ci gaba da aiwatar da manufofinta na inganta tsaro da haɗin gwiwa da ƙasashen duniya.
Ya ce wasiƙar ta ƙara ƙarfafa gwiwar gwamnati wajen ci gaba da ayyukan da take yi domin tabbatar da zaman lafiya da tsaron ƙasa.
