Majalisar Dattawan Najeriya ta amince da nadin Dr. Zainab Marwa a matsayin mamba a kwamitin gudanarwa na Hukumar Raya Yankin Neja Delta (NDDC), mai wakiltar shiyyar Arewa maso Gabas.
Amincewar ta biyo bayan nazari da kuma amincewa da rahoton Kwamitin Majalisar Dattawa kan NDDC a zaman majalisar na ranar Laraba.
Rahoton, wanda shugaban kwamitin, Sanata Ekpenyong Asuquo ya dauki nauyi, Sanata Patrick Ndubueze ne ya gabatar a gaban majalisar.
Ndubueze ya bayyana cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ne ya mika sunan Dr. Marwa ga majalisar domin tantancewa da amincewa, sannan aka tura batun ga kwamitin domin gudanar da bincike.
Ya ce kwamitin ya yi wa Dr. Marwa tantancewa tare da nazarin takardunta, inda ya tabbatar da cewa tana da kwarewa, nagarta da cancantar da ake bukata domin rike mukamin.
Bayan gabatar da rahoton, Majalisar Dattawa ta amince da nadinta ba tare da wata matsala ba.
Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya yabawa kwamitin bisa saurin kammala aikinsa, sannan ya taya Dr. Zainab Marwa murnar samun amincewar majalisar.
Akpabio ya bayyana fatan cewa gudunmawar Dr. Marwa za ta taimaka wajen bunkasa ci gaba da ayyukan raya yankin Neja Delta.
