Wasu ‘yan bindiga sun sace dalibai uku na Jami’ar Tarayya ta Lafia (FULafia) a daren Litinin a wani gidan haya da ake kira Living Seed Lodge, da ke wajen harabar jami’ar a Jihar Nasarawa.
Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Nasarawa ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce an samu kiran gaggawa daga Babban Jami’in Tsaro na jami’ar cewa wasu dauke da makamai sun yi awon gaba da daliban.
Bayan samun rahoton, Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar, Shetima Jauro Mohammed, ya tura jami’an sintiri da na musamman domin gudanar da aikin ceto a yankin dajin da ke kusa da wurin.
Kakakin rundunar, SP Ramhan Nansel, ya bayyana cewa aikin ceton ya yi nasarar kubutar da daya daga cikin daliban da aka sace, yayin da sauran biyu ke hannun masu garkuwa da su.
Rundunar ta ce an umarci dukkan sassan tsaro da na tattara bayanan sirri su ci gaba da aikin nema har sai an ceto sauran daliban cikin koshin lafiya tare da kamo wadanda suka aikata laifin.
‘Yan sanda sun bukaci mazauna yankin su kasance masu lura tare da kai rahoton duk wani motsi da ake zargi zuwa ofishin ‘yan sanda mafi kusa.
Rahotanni sun nuna cewa Living Seed Lodge na daga cikin gidajen daliban da ke wajen harabar jami’ar, kuma an taba samun makamantan hare-haren sace dalibai a irin wadannan wurare saboda karancin masaukin dalibai a jami’ar. Har yanzu ba a bayyana sunayen daliban da abin ya shafa ba, yayin da jami’an tsaro suka kara tsaurara sintiri a yankunan da dalibai ke zama.
