Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Legas ta gurfanar da fitaccen TikToker, Habeeb Hamzat, wanda aka fi sani da Peller, tare da abokinsa Bello Oladipo a gaban kotun majistare kan tuhume-tuhume guda uku da suka hada da hana jami’an ‘yan sanda gudanar da aikinsu, yin turjiya ga jami’an gwamnati da kuma daukar bidiyon jami’an yayin da suke bakin aiki.
Lamarin ya faru ne a ranar 2 ga Yuli, 2026, a titin Coastal Road da ke Lekki, Legas, bayan jami’an ‘yan sanda sun tare Peller bisa zargin tukin mota ba tare da lambar rajista ba.
Peller ya bayyana cewa sabuwar mota ce da ya saya, amma jami’an sun ce hakan ba hujja ba ce, tare da nacewa cewa dole ne a kai shi ofishin ‘yan sanda.
Rahotanni sun ce rikicin ya kara kamari ne bayan Peller ya fara daukar bidiyon mu’amalarsa da jami’an. Ya yi ikirarin cewa jami’an sun yi masa rashin mutunci, inda ya ce daya daga cikinsu ya ja rigarsa tare da yi masa barazanar bindiga.
Sai dai Rundunar ‘Yan Sanda ta gurfanar da Peller da Bello Oladipo a gaban kotu bisa zargin hada baki domin yin turjiya ga jami’an gwamnati da kuma hana ASP Agbede Victor da wasu jami’an uku gudanar da aikinsu yadda doka ta tanada.
Ana tuhumar su ne karkashin dokokin laifuffuka na Jihar Legas na shekarar 2015, kuma ana sa ran kotu za ta ci gaba da sauraron shari’ar a wani zama na gaba.
