Darakta Janar na hukumar da ake cece-kuce a kanta, Presidential Foreign Intervention Promotion Council (PFIPC), Adeniyi Adeyemi, ya bayyana cewa a shirye yake ya bai wa Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (ICPC) cikakken hadin kai domin gano gaskiyar lamarin.
Adeyemi ya bayyana hakan ne yayin wata hira da aka yi da shi a shafin Instagram, bayan umarnin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayar na gudanar da cikakken bincike kan hukumar cikin kwanaki 30.
Ya ce zai mika duk wasu takardun da ke hannunsa ga jami’an tsaro domin taimakawa binciken, yana mai cewa yana son a tantance sahihancin takardun tare da bankado gaskiyar abin da ya faru.
Adeyemi ya kuma yi mamakin yadda aka sanya PFIPC cikin kasafin kudin Najeriya na shekarar 2026 duk da cewa Fadar Shugaban Kasa ta ce ba ta taba kafa irin wannan hukuma ba. Ya ce bai da hannu a shigar da kasafin kudin saboda yana tsare a lokacin da ake shirya shi.
Dangane da zargin da ake yi wa Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Femi Gbajabiamila, Adeyemi ya ce ba zai zargi kowa ba, sai dai ya bukaci a gudanar da bincike mai zaman kansa domin gano gaskiya.
Shugaba Tinubu ya umarci ICPC ta binciki yadda aka kafa PFIPC, zargin amfani da takardun bogi wajen neman amincewar gwamnati, bude asusun bankuna da kuma hulda da ofisoshin jakadanci, tare da gabatar da rahoto cikin kwanaki 30.
A nata bangaren, Fadar Shugaban Kasa ta sake jaddada cewa PFIPC ba hukuma ba ce da Gwamnatin Tarayya ta kafa, yayin da binciken ‘yan sanda ya nuna cewa sa hannun da ke kan takardar nadin Adeyemi na bogi ne.
