Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Ebonyi ta fara bincike kan zargin da ake yi wa wasu jami’anta na Ofishin ‘Yan Sanda na Ohaukwu da dukan wani farar hula a karamar hukumar Ohaukwu.
Lamarin ya dauki hankalin jama’a ne bayan hotunan mutumin da aka ce an ci zarafinsa sun bazu a shafukan sada zumunta.
Wani mai amfani da shafin X mai suna @martins_nwede ya wallafa hoton mutumin tare da zargin cewa wani jami’in dan sanda mai suna Kingsley Esheya ne ya aikata hakan, yana kuma kira da a hukunta jami’in.
A cikin wata sanarwa da Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Ebonyi, SP Joshua Ukandu, ya fitar a ranar Talata, ya ce an gano jami’an da ake zargi, an tsare su, sannan an mayar da su hedikwatar rundunar jihar bisa umarnin Kwamishinan ‘Yan Sanda, Hope Okafor.
Sanarwar ta ce Kwamishinan ya kuma umurci Mataimakin Kwamishinan ‘Yan Sanda mai kula da Sashen Binciken Manyan Laifuka (SCID) da ya gudanar da cikakken bincike kan lamarin.
Rundunar ta bayyana cewa za a dauki matakin ladabtarwa da ya dace kan jami’an idan binciken ya tabbatar da laifinsu.
Ta kuma tabbatar da cewa mutumin da aka ci zarafinsa na samun kulawa a Asibitin Koyarwa na Tarayya da ke Abakaliki (FETHA), tare da yi masa fatan samun sauki cikin gaggawa.
Rundunar ta ba jama’a tabbacin cewa za a gudanar da binciken cikin gaskiya da adalci, tare da bin doka da ka’idoji.
Hakazalika, ta sake jaddada cewa ba za ta lamunci cin zarafin jama’a ko rashin da’a daga jami’anta ba, tana mai tabbatar da kudirinta na kare hakkin ‘yan kasa da tabbatar da kwarewa da rikon amana a aikin ‘yan sanda.
