Wata ‘yar Najeriya, Dakta Dorcas Akanbi, ta kammala karatun likitanci a wata jami’ar koyon aikin likita da ke kasar Rasha da maki 4.90 cikin 5.00 na CGPA, inda ta zama daya daga cikin fitattun daliban da suka yi fice a ajinsu.
Sabuwar likitar ta bayyana farin cikinta a wani sako da ta wallafa a shafinta na X a ranar 3 ga Yuli, tana gode wa Allah bisa nasarar da ta samu.
Ta rubuta cewa, “A karshe na zama cikakkiyar likita! Daga Jami’ar Legas (UNILAG) zuwa Rasha, Allah Ya yi.”
A wani sako na gaba, Akanbi ta wallafa bidiyon yadda ta gabatar da jawabin bankwana (valedictory speech) cikin kwarewa da harshen Rashanci a gaban malamai, jami’an jami’a, dalibai, iyalai da baki.
Jawabin nata ya samu tafi daga mahalarta taron, kuma ya jawo yabawa sosai a kafafen sada zumunta, inda mutane da dama suka yaba da kwarewarta a harshen Rashanci tare da taya ta murnar wannan gagarumar nasara.
Da take mayar da martani ga sakonnin taya murna da ta samu, Akanbi ta ce ba za ta iya amsa dukkan sakonnin ba saboda yawansu, amma tana matukar godiya ga kowa.
Ta kuma bayyana cewa tana alfahari da kasancewarta ‘yar Najeriya kuma za ta ci gaba da wakiltar kasarta da mutunci a duk inda take.
Nasarar Dakta Dorcas Akanbi ta samu yabo daga ‘yan Najeriya da dama a kafafen sada zumunta, inda suka bayyana ta a matsayin abin koyi ga matasa da kuma mutum mai daukaka sunan Najeriya a idon duniya.
