Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Akwa Ibom ta kama wasu mutane uku da ake zargin mambobin kungiyar asiri ta Vikings Confraternity ne a wani samame da jami’anta suka kai bayan samun sahihan bayanan sirri a wani gida da ke kan titin Abak Road a birnin Uyo.
Mutanen da aka kama sun hada da Dick Udofia, Emem Charles da Ubong Matthew.
A cewar rundunar, an samu wasu abubuwan da ake zargin kwayoyi ne a hannunsu, ciki har da methamphetamine (Ice), wiwi da sauran kayayyakin da ake amfani da su wajen shan miyagun kwayoyi.
Mai magana da yawun rundunar, Timfon John, ta bayyana a cikin wata sanarwa cewa mutanen uku sun amsa cewa su mambobin kungiyar asiri ta Vikings ne.
Ta kara da cewa dukkansu dalibai ne a wata kwalejin fasaha (Polytechnic), amma ba a bayyana sunan makarantar ba saboda dalilan bincike.
Binciken farko ya nuna cewa daya daga cikin wadanda aka kama, Ubong Matthew, an tilasta masa shiga kungiyar a ranar 5 ga Yuli, 2026, a wani biki da ake zargin Dick Udofia ne ya shirya a wannan gida.
Rundunar ta ce wadanda ake zargin na ci gaba da bai wa jami’an tsaro bayanan da za su taimaka wajen cafke sauran wadanda suka tsere.
A wani lamari daban, rundunar ta kuma kama wani jami’in tsaro mai zaman kansa mai suna Joshua Akpan, mai shekaru 32, bisa zargin satar da lalata manyan wayoyin lantarki masu sulke daga coci-coci, gidajen zama, masana’antu da wasu gine-ginen gwamnati.
Bincike a gidansa ya kai ga gano wayoyin lantarki da aka yanke, tarin wayoyin da aka cire daga wurare daban-daban, filaya, abin yankan karfe, guduma da sauran kayan aikin da ake zargin ana amfani da su wajen aikata laifin.
A cewar ‘yan sanda, Joshua Akpan ya amsa cewa ya sace wayoyin lantarki daga babban cocin Catholic Cathedral, inda yake aiki a matsayin jami’in tsaro.
Rundunar ta ce bincike na ci gaba domin cafke sauran mambobin kungiyar da ake zargi da hannu a laifukan tare da kwato sauran kayayyakin da aka sace.
