Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta tabbatar da Sanata David Mark a matsayin shugaban jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), bayan ta yi watsi da karar da dan majalisar wakilai, Leke Abejide, ya shigar yana kalubalantar sabon shugabancin jam’iyyar.
Mai shari’a Justice Musa Liman ya yanke hukuncin cewa karar ba ta da tushe a doka, domin ta shafi harkokin cikin gida na jam’iyyar siyasa, wadanda kotu ba ta da hurumin tsoma baki a cikinsu sai idan an karya doka ko an take hakkin wani.
Kotun ta kuma amince da bukatar farko da ADC da tsohon shugaban jam’iyyar Ralph Nwosu, shugaban na yanzu David Mark, da sakataren jam’iyyar Rauf Aregbesola suka gabatar.
Alkalin ya ce Abejide bai nuna cewa an take masa wani hakki na doka ba, sannan bai bi hanyoyin warware rikici na cikin jam’iyyar kafin ya garzaya kotu ba.
A hukuncin, kotun ta bayyana cewa sauyin shugabanci daga Ralph Nwosu zuwa David Mark bai saba wa kundin tsarin mulkin jam’iyyar ADC ko kuma Dokar Zabe ba.
Haka kuma, kotun ta ce taron masu ruwa da tsaki na ranar 2 ga Yuli, 2025, da taron kwamitin zartarwa na jam’iyyar (NEC) na 29 ga Yuli, 2025, sun kasance sahihin tsarin da ya haifar da nada David Mark a matsayin shugaban jam’iyyar da Rauf Aregbesola a matsayin sakatare.
Kotun ta kuma lura cewa Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta sanya ido kan taron NEC, wanda ya kara tabbatar da sahihancin tsarin.
Saboda haka, kotun ta yi watsi da dukkan bukatun da Abejide ya gabatar tare da tabbatar da halaccin shugabancin David Mark da Rauf Aregbesola.
Bugu da kari, kotun ta umarci Abejide ya biya kowanne daga cikin wadanda ake kara Naira miliyan 2 a matsayin kudin shari’a, sannan ta ci tarar lauyansa Naira miliyan 10 bisa tanadin Dokar Zabe.
