Gwamnatin Tarayya ta tabbatar da shirinta na sauya kayan khaki na masu yi wa kasa hidima (NYSC) da tufafin Adire da ake kera wa a Najeriya, a matsayin wani bangare na gyaran tsarin shirin.
Ministan Matasa, Ayodele Olawande, ne ya bayyana hakan yayin wata hira da gidan talabijin na Channels Television, inda ya ce matakin zai bunkasa masana’antar cikin gida tare da tabbatar da cewa kudaden gwamnati na tallafawa tattalin arzikin Najeriya.
A cewarsa, ana samar da kayan Adire a jihohi kamar Ogun da Kwara, don haka ya dace gwamnati ta rika amfani da kayayyakin da ake kerawa a cikin kasa.
Ministan ya kuma bayyana cewa a karkashin sabon tsarin, za a rika tura masu yi wa kasa hidima wuraren aiki bisa fannin karatun da suka yi. Misali, wadanda suka karanci ilimin koyarwa za a fi tura su makarantu domin amfani da kwarewarsu.
Dangane da tsaro, Olawande ya ce gwamnati na duba yiwuwar tura matasa zuwa yankunan da suka yi karatu ko kuma suka saba da muhallinsu, musamman a wuraren da ke fuskantar matsalolin tsaro, domin rage damuwar iyaye da kuma saukaka tsarin tura masu hidimar kasa.
Ya kuma karyata rahotannin da ke cewa za a cire rundunar soji daga shirin NYSC, yana mai cewa sojoji za su ci gaba da bayar da tsaro ga masu yi wa kasa hidima a fadin Najeriya.
Sauye-sauyen na zuwa ne bayan Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) ta amince da babban garambawul ga tsarin NYSC, wanda ya hada da gyaran dokar shirin domin dacewa da sabbin tsare-tsaren da gwamnati ta amince da su.
