Jam’iyyar PDP a Jihar Kwara ta bayyana Fasto Cornelius Fawenu, tsohon Sakataren Kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) a jihar, a matsayin mataimakin dan takarar gwamna na jam’iyyar domin zaben shekarar 2027.
Dan takarar gwamnan jam’iyyar, Injiniya Suleiman Kawu, ne ya mika sunan Fawenu ga shugaban PDP na jihar a cikin wata wasika, bayan gudanar da tattaunawa da shugabannin jam’iyya da masu ruwa da tsaki daga dukkan shiyyoyin sanatoci uku na jihar.
A cikin wasikar, Kawu ya bayyana Fawenu a matsayin mutum mai gaskiya, tawali’u, tausayi da kuma kwarewa wajen jagoranci, yana mai cewa ya cancanci zama abokin takararsa.
A wata sanarwa da Sakataren Yada Labarai na PDP a jihar, Olusegun Adewara, ya sanya wa hannu, jam’iyyar ta ce zaben Fawenu ya biyo bayan dogon nazari da shawarwari tare da manyan jiga-jigan jam’iyyar.
Sanarwar ta kara da cewa jam’iyyar na sanar da al’ummar Kwara da ma ‘yan jihar da ke zaune a kasashen waje cewa an gudanar da zabin mataimakin dan takarar ne cikin gaskiya da tuntuba domin tabbatar da hadin kai a gabanin zaben gwamnan jihar na shekarar 2027.
