Dakarun Operation FANSAN YAMMA na Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa maso Yamma sun ƙara zafafa farmaki kan ‘yan ta’adda da masu garkuwa da mutane, inda suka kashe mutum biyu da ake zargin ‘yan ta’adda ne, suka ceto mutum ɗaya da aka yi garkuwa da shi, suka kama wasu mutum takwas da ake zargin masu haɗa baki ne, tare da kwato shanu 110 da aka sace.
Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da Jami’in Yaɗa Labarai na rundunar, Laftanar Kanar Aliyu Danja, ya fitar, inda ya ce an gudanar da ayyukan tsakanin ranar 27 zuwa 28 ga Yuni, 2026 a jihohin Kaduna da Zamfara.
Sanarwar ta bayyana cewa dakarun Sector 1, tare da haɗin gwiwar jami’an tsaro na sa-kai, sun yi artabu da wasu ‘yan ta’adda da ke jigilar mutanen da suka yi garkuwa da su a kan babura a ƙananan hukumomin Giwa da Kaduna North na Jihar Kaduna.
Bayan musayar wuta mai zafi, ‘yan ta’addan sun yi watsi da babura biyu tare da tserewa cikin daji. Dakarun sun ceto mutum ɗaya da aka yi garkuwa da shi da ransa, yayin da suka gano gawar wani wanda aka yi zargin ‘yan ta’addan sun kashe kafin su tsere.
A wani farmaki da aka kai daga baya a ranar, dakarun sun garzaya ƙauyen Dariya da ke Ƙaramar Hukumar Giwa bayan samun rahoton harin ‘yan ta’adda.
Rahotanni sun nuna cewa maharan sun kashe farar hula guda ɗaya tare da jikkata wasu uku kafin jami’an tsaro su isa wurin.
Yayin da ‘yan ta’addan ke ƙoƙarin tserewa a kan babura, dakarun sun sake fafatawa da su, inda suka kashe biyu daga cikinsu tare da ƙwato babur, harsasai, laya da wasu kayayyaki.
A wani samame na bayanan sirri da aka gudanar a Magami da ke Ƙaramar Hukumar Gusau ta Jihar Zamfara, dakarun Sector 2 sun kama mutum biyu da ake zargin suna ba ƙungiyoyin ‘yan ta’adda magunguna da kulawar lafiya.
Haka kuma, a yankin Pole Wire Village da ke Ƙaramar Hukumar Birnin Gwari ta Kaduna, an kama wasu mutum shida da aka tarar cikin yanayi mai tayar da zargi jim kaɗan bayan artabu da wasu ‘yan ta’adda masu tserewa.
Rundunar ta ce ana ci gaba da binciken waɗanda aka kama.
A ranar 28 ga Yuni, dakarun tare da haɗin gwiwar jami’an tsaro na sa-kai sun kuma dakile wani yunƙurin satar shanu a Ƙaramar Hukumar Chikun ta Jihar Kaduna.
Bayan bin sawun masu satar shanun da kuma kafa kwanton ɓauna a hanyar da ake zargin za su bi, barayin sun yi watsi da dabbobin tare da tserewa sakamakon matsin lambar da jami’an tsaro suka yi musu.
An kwato shanu 110 baki ɗaya tare da mayar da su ga masu su.
Rundunar Operation FANSAN YAMMA ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da kai hare-hare kan ‘yan ta’adda da sauran masu aikata laifuka domin tabbatar da zaman lafiya da kare rayuka da dukiyoyin al’umma a yankin Arewa maso Yammacin Najeriya.
Ta kuma yi kira ga jama’a da su ci gaba da bai wa jami’an tsaro sahihan bayanan sirri cikin lokaci domin taimakawa wajen yaƙi da matsalar tsaro.
