Gwamnan Jihar Taraba, Agbu Kefas, ya bayyana cikakken goyon bayansa ga shirin kafa rundunar ‘yan sandan jihohi (State Police), yana mai cewa hakan muhimmin mataki ne na ƙarfafa tsarin tsaron Najeriya.
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da ya karɓi Mataimakin Sufeto Janar na ‘Yan Sanda (DIG) mai kula da Force Intelligence Department, Zachariah Fera Achinyan, da DIG mai kula da shiyyar Arewa maso Gabas, Ibrahim Babazango, a wata ziyarar ban girma da suka kai masa a gidan gwamnatin TY Danjuma House da ke Jalingo.
Kefas ya ce an riga an gudanar da tattaunawa mai zurfi kan batun kafa ‘yan sandan jihohi, yana mai bayyana kwarin gwiwar cewa gwamnonin jihohi za su bayar da gudunmawa mai ma’ana domin tabbatar da nasarar aiwatar da tsarin.
Ya jaddada cewa ƙarfafa hukumomin tsaro na da matuƙar muhimmanci wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Gwamnan ya kuma sake tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da ba Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya da sauran hukumomin tsaro cikakken goyon baya domin yaƙi da aikata laifuka da tabbatar da zaman lafiya a faɗin Jihar Taraba.
Tun da farko, DIG Zachariah Fera Achinyan ya bayyana cewa Sufeto Janar na ‘Yan Sandan Najeriya, Olstunji Rilwan Disu, ya umarci manyan jami’an rundunar su kai ziyara zuwa shiyyoyi shida na ƙasar domin duba shirye-shiryen hukumomin tsaro wajen fuskantar sabbin barazanar tsaro.
A cewarsa, ziyarar na da nufin tantance yadda rundunonin ‘yan sanda ke shirin tunkarar matsalolin tsaro, ƙarfafa tattara bayanan sirri da kuma inganta haɗin gwiwa tsakanin ‘yan sanda da gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki.
DIG Achinyan ya jaddada cewa ci gaba da haɗin kai tsakanin hukumomin tsaro, gwamnati da al’umma shi ne ginshiƙin yaƙi da aikata laifuka da tabbatar da tsaron jama’a.
Ya kuma yabawa Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Taraba bisa nasarorin da ta samu wajen yaƙi da masu aikata laifuka, yana mai cewa ziyararsa na da nufin ƙarfafa waɗannan nasarori da kuma tabbatar da dorewar zaman lafiya da tsaro a jihar.
