Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, , ya rantsar da sabbin sanatoci hudu bayan nasararsu a zabukan ciko gurbi da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta gudanar kwanan nan.
Sabbin sanatocin sun hada da na jam’iyyar PDP mai wakiltar mazabar Rivers South-East, na jam’iyyar APC mai wakiltar Nasarawa North, na APC mai wakiltar Enugu North, da kuma na APC mai wakiltar Ondo South.
An gudanar da bikin rantsar da su ne bayan zabukan ciko gurbi da aka gudanar a ranar Asabar domin maye gurbin kujerun da suka zama babu kowa a wasu mazabun sanatoci.
Kujerar Rivers South-East ta zama babu kowa ne bayan rasuwar tsohon Sanata .
Haka kuma, Anza ya lashe kujerar Nasarawa North bayan rasuwar tsohon Sanata .
A jihar Enugu kuwa, Asogwu ya maye gurbin marigayi , yayin da Faduyile ya cike gurbin da ya biyo bayan nadin tsohon Sanata a matsayin wakilin Najeriya na dindindin a Majalisar Dinkin Duniya.
Rantsar da sabbin sanatocin na nufin cike gibin wakilci da aka samu a wadannan mazabu, tare da tabbatar da ci gaba da gudanar da ayyukan majalisar ba tare da tangarda ba.
