Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta mika takardun shaidar cin zabe ga wadanda suka yi nasara a zabukan cike gurbi da aka gudanar a jihohin Rivers, Enugu, Nasarawa, Ondo da Kano a ranar 20 ga Yunin 2026.
An mika takardun ne a madadin Shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan (SAN), ta hannun Kwamishiniyar Hukumar da ke kula da Jihar Rivers, Hajiya May Agbamuche-Mbu.
A yayin bikin mika takardun, Agbamuche-Mbu ta taya wadanda suka yi nasara murna tare da jaddada musu muhimmancin wakiltar al’ummarsu yadda ya kamata.
Ta ce babban nauyin da ke kansu shi ne tabbatar da cewa sun kare muradun jama’ar da suka zabe su tare da yi musu aiki da gaskiya da rikon amana.
Ta kuma bayyana cewa za a mika irin wadannan takardu ga wadanda suka yi nasara a zaben mazabar Zuru ta Jihar Kebbi da kuma zaben gwamnan Jihar Ekiti.
Rahotanni sun nuna cewa jam’iyyar APC ta samu gagarumar nasara a zabukan cike gurbin da aka gudanar, inda ta lashe kujeru a jihohin Ondo, Nasarawa, Kano da Kebbi.
Sai dai jam’iyyar PDP ta ci gaba da rike kujerar Sanatan Rivers South-East bayan ta samu nasara a zaben yankin.
Duk da nasarorin da aka samu, wasu daga cikin zabukan sun fuskanci zarge-zargen magudi, tashin hankali da kuma tsoratar da masu kada kuri’a, lamarin da ya jawo ce-ce-ku-ce daga bangarori daban-daban.
