Wasu ‘yan takarar gwamnan jihar Kwara guda 10 na jam’iyyar APC sun yi kira ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya hana amfani da sarakunan gargajiya wajen neman amincewa da dan takarar gwamna na jam’iyyar a jihar, Salihu Danladi.
A cikin wata budaddiyar wasika da suka aikewa shugaban kasar, ‘yan takarar sun bayyana damuwarsu kan rahotannin da ke cewa ana shirin kai wasu sarakunan gargajiya masu daraja daga Kwara zuwa fadar shugaban kasa domin nuna goyon baya ga Danladi, wanda ya lashe zaben fidda gwani na APC a watan Mayun 2026.
Sun ce har yanzu akwai korafe-korafe da dama game da yadda aka gudanar da zaben fidda gwanin, don haka bai dace a yi amfani da sarakunan gargajiya wajen tabbatar da sahihancin sakamakon zaben ba.
Masu sanya hannu a wasikar sun hada da Dele Belgore (SAN), Ambasada Yahaya Gambari, Sanata Saliu Mustapha, Sanata Yahaya Oloriegbe, Dakta Oluwatoyin Alabi, Alhaji Tajudeen Audu, Omar Bio, Dakta Bashir Bolarinwa, Kyaftin Ahmad Mahmud da Dakta Azeez Olaniyi.
Sun jaddada cewa suna girmama sarakunan gargajiya kuma suna ganin su a matsayin masu kare al’adu da martabar al’umma, amma suka ce bai kamata a jawo su cikin takaddamar siyasa ba saboda hakan na iya rage darajarsu da matsayinsu na masu zaman kansu.
‘Yan takarar sun kuma bayyana cewa irin wannan ziyara na iya haifar da tunanin cewa dukkan masu ruwa da tsaki a APC ta Kwara sun amince da sakamakon zaben fidda gwani, alhali akwai masu adawa da yadda aka gudanar da shi.
Baya ga haka, sun yi tambaya kan dalilin da ya sa ba a taba hada irin wannan tawagar sarakuna domin neman taimakon gwamnatin tarayya kan matsalolin tsaro da ke addabar wasu yankunan jihar ba.
Sun ce yankuna da dama a kananan hukumomin Baruten, Kaiama, Patigi, Edu, Ifelodun, Irepodun da Isin na fama da matsalolin tsaro, amma ba a ga wata irin gagarumar tawagar sarakuna da ta kai koke kan lamarin ba.
A karshe, sun bukaci Shugaba Tinubu da ya tabbatar da adalci, gaskiya da bin ka’idojin dimokuradiyya a cikin harkokin jam’iyyar APC domin karfafa hadin kai da zaman lafiya a jihar Kwara.
