An samu cunkoson ababen hawa mai tsanani a mashahuriyar mahadar Iwo Road da ke Ibadan, babban birnin Jihar Oyo, bayan wasu masu zanga-zanga sun tare hanyar a safiyar Litinin.
Masu zanga-zangar sun taru a yankin da misalin karfe 10 na safe karkashin jagorancin kungiyar kare hakkin dan Adam ta Take It Back Movement.
Masu zanga-zangar na neman kawo karshen matsalar rashin tsaro a kasar nan tare da kira ga hukumomi da su tabbatar da ceto dalibai da malamai 39 da aka sace a Jihar Oyo.
Yayin da yake magana da manema labarai, Kodinetan kungiyar na kasa, Juwon Sanyaolu, ya bayyana cewa zanga-zangar wani bangare ne na ci gaba da matsin lambar da kungiyar ke yi tun bayan sace dalibai da malamai a Karamar Hukumar Oriire ta Jihar Oyo a watan Mayu.
Sanyaolu ya ce kungiyar ta himmatu wajen ganin an kubutar da wadanda aka sace tare da jawo hankalin gwamnati da jami’an tsaro kan matsalar tsaro da ke kara kamari a sassan kasar.
A cewarsa, rashin daukar matakan gaggawa kan lamarin ne ya sa suka sake fitowa domin nuna damuwa da kuma neman mafita mai dorewa.
Taron ya jawo cunkoso mai yawa a mahadar Iwo Road, daya daga cikin hanyoyin da suka fi hada zirga-zirga a Ibadan, inda direbobi da matafiya suka shafe lokaci mai tsawo suna jiran bude hanya.
Masu zanga-zangar sun yi ta rera wakoki tare da dauke da alluna masu dauke da sakonnin kira ga gwamnati da ta kara kaimi wajen magance matsalar tsaro da kuma tabbatar da dawo da wadanda aka sace cikin koshin lafiya.
Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, jami’an tsaro na sa ido kan lamarin domin tabbatar da zaman lafiya da kauce wa duk wani tashin hankali yayin gudanar da zanga-zangar.
