Hukumar gudanarwar Asibitin Koyarwa na Tarayya da ke Gombe (FTH Gombe) ta roki al’umma da su taimaka wajen gano ko nemo iyalan wani mutum da ya rasu sakamakon hatsarin mota, wanda har yanzu babu wanda ya zo ya karɓi gawarsa a ma’ajiyar gawa ta asibitin.
A cikin wata sanarwa da sashen hulɗa da jama’a na asibitin ya fitar a ranar Juma’a, an bayyana cewa mamacin namiji ne mai kimanin shekaru 35 da haihuwa, wanda ya yi hatsari a yankin Government Reserved Area (GRA) da ke Jihar Gombe.
Sanarwar ta ce wani jami’in Hukumar EFCC ne ya kai mutumin asibitin bayan wata mota da ta gudu ta buge shi a kan hanya.
An kwantar da shi a asibitin ranar 15 ga Mayu, 2026, amma abin takaici ya rasu bayan kwana biyu, wato ranar 17 ga Mayu, 2026.
Asibitin ya bayyana cewa mamacin yana da tsayin santimita 155.4 kuma yana da wasu alamomin gargajiya na kwance a kumatunsa biyu, waɗanda za su iya taimakawa wajen gane shi.
Asibitin ya ce duk da ƙoƙarin da aka yi na nemo danginsa, har yanzu babu wani ɗan uwa da ya bayyana domin karɓar gawarsa.
Saboda haka, an bukaci duk wanda ya san mamacin ko yake da wani bayani game da shi ko iyalansa da ya tuntubi hukumomin asibitin domin a kammala matakan da suka dace.
Wannan kira na zuwa ne yayin da ake ci gaba da fuskantar matsalar gawarwakin mutanen da suka mutu a hatsura daban-daban, waɗanda ke ci gaba da zama a ma’ajiyun gawa saboda rashin gano iyalansu.
