Gwamnatin Jihar Enugu ta sanar da hana zirga-zirga a dukkan kananan hukumomi shida da suka hada da yankin Sanatan Enugu ta Arewa gabanin zaben cike gurbi da za a gudanar ranar Asabar.
Sakataren Gwamnatin Jihar, Farfesa Chidiebere Onyia, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwar jama’a da aka fitar ranar Juma’a.
A cewarsa, dokar hana zirga-zirgar za ta shafi dukkan gundumomin zabe 102 da ke cikin yankin Sanatan Enugu ta Arewa.
Sanarwar ta ce za a fara aiwatar da dokar ne daga karfe 6:00 na safe zuwa karfe 4:00 na yamma a ranar Asabar, 20 ga Yunin 2026, domin tabbatar da zaman lafiya da gudanar da sahihin zabe.
“Gwamnatin Jihar Enugu na sanar da jama’a cewa za a gudanar da zaben cike gurbi na Sanatan Enugu ta Arewa ranar Asabar, 20 ga Yunin 2026. Domin tabbatar da zaman lafiya, tsari da kuma sahihancin zaben, za a hana zirga-zirga daga karfe 6:00 na safe zuwa 4:00 na yamma a dukkan kananan hukumomi shida da gundumomin zabe 102 da ke yankin,” in ji sanarwar.
Sai dai gwamnatin ta ware jami’an Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), jami’an tsaro, masu sa ido kan zabe da aka tantance, ‘yan jarida da sauran mutanen da aka ba izinin gudanar da ayyukan da suka shafi zaben daga cikin wadanda dokar za ta shafa.
Gwamnatin ta bukaci mazauna yankin da masu kada kuri’a su gudanar da harkokinsu cikin lumana tare da bin dokoki da ka’idojin zabe.
Haka kuma ta yi kira ga jam’iyyun siyasa, ‘yan takara da magoya bayansu da su kasance masu bin doka kafin zabe, yayin gudanar da shi da kuma bayan an kammala.
Onyia ya ce an umarci jami’an tsaro su tabbatar da bin wannan umarni tare da kula da zaman lafiya da doka a duk lokacin gudanar da zaben.
Ya kara da cewa jama’ar yankin su yi amfani da damar da kundin tsarin mulki ya ba su wajen kada kuri’a cikin lumana da bin ka’idojin da aka gindaya.
Gwamnatin jihar ta kuma gode wa mazauna yankin bisa fahimta da hadin kai da suke bayarwa, tare da yi musu fatan samun nasarar gudanar da zaben cikin lumana.
Yankin Sanatan Enugu ta Arewa ya kunshi kananan hukumomin Igbo-Etiti, Igbo Eze North, Igbo Eze South, Nsukka, Udenu da Uzo-Uwani.
Hukumar INEC ce ke gudanar da zaben cike gurbin domin maye gurbin kujerar Sanatan yankin da ta zama babu mai Irike da ita.
