Ma’aikatar Ilimi, Kimiyya da Fasaha ta Jihar Ogun ta fitar da sabon umarni da ke haramta gudanar da bukukuwan kammala karatu ga daliban Nursery, Kindergarten da sauran azuzuwan da ba na karshe ba a dukkan makarantun gwamnati da masu zaman kansu a jihar.
Sabon umarnin, mai lamba PRVS 426/5 kuma mai dauke da kwanan watan 18 ga Yunin 2026, an aike shi ne ga shugabannin makarantu ta hannun jami’an kula da yankunan ilimi.
Ma’aikatar ta bayyana cewa matakin na daga cikin kokarin rage wa iyaye da masu kula da yara nauyin kudaden da ake kashewa wajen shirya irin wadannan bukukuwa.
Takardar umarnin, wacce Daraktan Ilimi na Makarantu Masu Zaman Kansu, Bisiriyu A.A., ya sanya wa hannu a madadin Sakataren Dindindin na ma’aikatar, ta bayyana cewa daga yanzu bukukuwan kammala karatu za su takaita ne kawai ga daliban aji shida na firamare (Primary Six), JSS 3 da kuma SSS 3.
A cewar ma’aikatar, wadannan rukunan dalibai ne kawai ake dauka suna kammala wani muhimmin mataki na karatu a tsarin ilimi.
Sai dai ko ga wadannan azuzuwan, an umurci makarantu da su gudanar da bukukuwan cikin sauki ba tare da kakaba wa iyaye ko dalibai wani nauyin kudi ba.
Har ila yau, ma’aikatar ta haramta duk wasu abubuwan da ta bayyana a matsayin almubazzaranci yayin bukukuwan kammala karatu.
Takardar ta ce amfani da tantuna, Aso Ebi, tufafin musamman da aka kera domin bikin ko wasu nau’ikan nuna isa da kashe kudade fiye da kima a irin wadannan taruka an haramta su gaba daya.
Ma’aikatar ta bukaci masu makarantu da shugabanninsu su mayar da hankali kan yabawa kokarin dalibai a bangaren karatu da tarbiyya maimakon shirya bukukuwa masu tsada da ke kara wa iyaye nauyin kudi.
Ta kuma umurci dukkan makarantu da su tabbatar da cewa an yada wannan umarni ga kowa tare da bin sa ba tare da karya ka’ida ba.
Gwamnatin jihar ta yi gargadin cewa duk makarantar da aka samu da karya wannan doka za ta fuskanci hukunci kamar yadda dokokin gudanar da makarantu a jihar suka tanada.
Tun da farko, gwamnatin Ogun ta taba fitar da wani umarni da ya dakatar da bukukuwan kammala karatu da kuma bukukuwan karshen zangon karatu a makarantun gwamnati da masu zaman kansu.
A wancan lokaci, gwamnati ta bayyana cewa wasu makarantu na amfani da irin wadannan bukukuwa wajen karbar kudade masu yawa daga iyaye da masu kula da yara.
Saboda haka, gwamnatin ta ce sabon matakin na da nufin kare iyaye daga matsin tattalin arziki da kuma tabbatar da cewa harkar ilimi ba ta zama wata hanya ta karin nauyin kudi ga iyalai ba.
