Wani dan takarar Sanata a karkashin jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC), Nwachukwu, ya maka jam’iyyar da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) a kotu, yana neman a tabbatar da shi a matsayin halastaccen dan takarar Imo North Senatorial Zone a zaben shekarar 2027.
A cikin karar da ya shigar, Nwachukwu ya bukaci kotu ta bayyana cewa shi ne dan takarar hadin kai (consensus candidate) na jam’iyyar NDC a yankin Imo North kuma a hana jam’iyyar gabatar da wani daban a zaben Sanata na shekarar 2027.
Har ila yau, ya nemi kotu ta hana INEC amincewa ko karbar sunan wani mutum a matsayin dan takarar NDC a yankin har sai an yanke hukunci kan karar da ke gaban kotu.
A cikin takardar rantsuwar da ya gabatar tare da karar, Nwachukwu ya zargi jam’iyyar da aikata kura-kurai da saba ka’idojinta tun daga matakin tantance ‘yan takara.
Ya ce daya daga cikin abubuwan da suka nuna rashin daidaito shi ne yadda kudin tallafin jam’iyya da ya biya na Naira miliyan 20 aka danganta su da wani dan takara mai suna Matthew Omegara, yayin da kudin Naira miliyan 10 da Omegara ya biya aka danganta su da shi.
Nwachukwu ya bayyana cewa ya bi umarnin jam’iyyar ta hanyar shiga tantancewar ‘yan takara kuma an amince da shi ya shiga zaben fidda gwani.
Ya kara da cewa ya sayi fom din nuna sha’awar tsayawa takarar Sanatan Imo North tare da bayar da gudunmawar Naira miliyan 20 domin tallafawa jam’iyyar.
A cewarsa, bayan an amince da shi a matsayin dan takarar hadin kai, an sanya sunansa cikin jerin ‘yan takarar da suka yi nasara kuma aka tabbatar da shi a matsayin wanda zai wakilci jam’iyyar a yankin.
Sai dai ya yi zargin cewa daga baya an cire sunansa tare da maye gurbinsa da wani dan takara duk da cewa shi ne ya lashe zaben fidda gwani.
Nwachukwu ya kuma yi ikirarin cewa shugaban jam’iyyar na kasa, Sanata Seriake Dickson, ya gayyace shi wani taro inda aka sanar da shi cewa wasu shugabannin jam’iyyar daga jihar Imo sun nuna cewa ba shi da farin jini sosai da zai iya wakiltar jam’iyyar a zaben Sanata.
Saboda haka, ya bukaci kotu ta tilasta wa NDC ta ba shi takardar shaidar nasara (Certificate of Return) a matsayin dan takarar jam’iyyar na Imo North Senatorial District a zaben 2027.
Da aka tuntubi kakakin jam’iyyar NDC a jihar Imo, Dakta Charles Akano, ya ce yana bukatar samun izini daga shugabannin jam’iyyar kafin ya yi magana kan lamarin.
Bayan sa’o’i uku, Akano ya sake bayyana cewa har yanzu bai samu izinin yin tsokaci kan batun ba.
Ya ce ya yi kokarin tuntubar shugabannin jam’iyyar a jihar Imo amma ba su amsa kiransa ba, don haka ba zai iya yin karin bayani kan lamarin a halin yanzu ba.
