Hedikwatar Tsaro ta Kasa (DHQ) ta tabbatar wa iyalan marigayi Manjo Janar Rabe Abubakar mai ritaya cewa jami’an tsaro za su tabbatar an kamo tare da hukunta wadanda ke da hannu a mutuwarsa.
Wannan tabbacin ya fito ne yayin da wata tawaga daga DHQ karkashin jagorancin Babban Jami’in Gudanarwa na Sojojin Kasa, Manjo Janar IM Abdullahi, ta kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan marigayin da kuma Gwamnatin Jihar Katsina.
Tawagar ta isar da sakon ta’aziyyar Babban Hafsan Tsaron Kasa, Janar OO Oluyede, da daukacin rundunar sojojin Najeriya ga iyalan marigayin da al’ummar Jihar Katsina bisa wannan babban rashi.
Da yake jawabi a gidan marigayin, Manjo Janar Abdullahi ya bayyana Rabe Abubakar a matsayin jajirtaccen soja wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen bautawa kasa tsawon shekaru da dama.
Ya ce marigayin ya bayar da gagarumar gudunmawa wajen bunkasa rundunar sojin Najeriya da kuma harkokin tsaron kasa, inda ya yi aiki cikin kwarewa da kishin kasa.
Abdullahi ya kara da cewa rundunar sojoji da sauran hukumomin tsaro ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen gano tare da kamo wadanda suka haddasa mutuwar tsohon jami’in sojan.
Marigayi Manjo Janar Rabe Abubakar, wanda ya taba rike mukamin Daraktan Yada Labarai na Ma’aikatar Tsaro, ya rasu ne bayan shafe lokaci a hannun masu garkuwa da mutane da suka sace shi tare da matarsa a Jihar Katsina kusan makonni biyu da suka gabata.
Gwamnatin Jihar Katsina ta sanar da rasuwarsa a ranar Asabar, inda ta bayyana cewa ya mutu ne sakamakon tabarbarewar lafiyarsa yayin da yake tsare a hannun masu garkuwa da mutane.
An yi jana’izarsa a Katsina a ranar Asabar tare da halartar manyan jami’an gwamnati, na tsaro da dimbin al’umma.
DHQ ta jaddada cewa za ta ci gaba da mara wa iyalan marigayin baya tare da tabbatar da cewa an yi adalci kan wannan lamari mai tayar d8a hankali
