Gwamnatin Jihar Zamfara ta dakatar da Shugaban Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Abdu Gusau Polytechnic, Dakta Sirajo Shinkafi, daga mukaminsa nan take bisa zargin rashin da’a da kuma bijirewa umarnin gwamnati.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Jihar Zamfara, Abubakar Nakwada, ya fitar a ranar Litinin, inda ya bayyana cewa an dauki matakin ne domin tabbatar da ci gaba da gudanar da harkokin makarantar cikin tsari da kwanciyar hankali.
Sanarwar ta ce gwamnatin jihar ta dauki matakin dakatarwar ne domin ba da damar gudanar da ayyukan ilimi da na gudanarwa ba tare da tangarda ba, tare da tabbatar da cewa ayyukan makarantar ba za su tsaya ba.
Nakwada ya kara da cewa gwamnati ta riga ta tanadi matakan da za su tabbatar da ci gaba da tafiyar da harkokin makarantar yadda ya kamata yayin da ake gudanar da bincike kan lamarin.
Sai dai kokarin jin ta bakin Dakta Sirajo Shinkafi ya ci tura, domin wayarsa ba ta shiga ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto.
Gwamnatin Zamfara ta tabbatar wa al’ummar makarantar da jama’ar jihar cewa za ta ci gaba da daukar matakan da suka dace domin tabbatar da ingantaccen tsarin gudanarwa a cibiyoyin gwamnati.
