Majalisar Wakilai ta Kasa ta kawo karshen burin dan majalisar mai wakiltar mazabar Ideato ta Arewa da Kudu a jihar Imo, Ikenga Ugochinyere, na zama Jagoran ‘Yan Adawa (Minority Leader) bayan amincewa da sabon fassarar ka’idar gogewar aikin majalisa.
Matakin ya biyo bayan amincewa da kudirin da dan majalisa mai wakiltar Ikorodu a jihar Legas, Babajimi Benson, ya gabatar a zaman majalisar da Kakakin Majalisar, Tajudeen Abbas, ya jagoranta.
Mukamin Jagoran ‘Yan Adawa ya zama babu mai rike da shi ne bayan tsohon mai mukamin, Kingsley Chinda, ya fice daga jam’iyyar adawa zuwa APC tare da zama dan takarar gwamna a jihar Rivers domin zaben 2027.
Ugochinyere, wanda aka fara zaba a majalisar a shekarar 2023, ya samu goyon bayan wasu ‘yan majalisa da dama domin neman mukamin. Sai dai sabuwar dokar da majalisar ta tabbatar ta bayyana cewa sai dan majalisar da ya kammala cikakken wa’adin shekaru hudu a majalisa kafin ya cancanci rike mukamin jagoranci.
Majalisar ta ce babu wata ma’ana ta “gogewar aikin majalisa” face kasancewa mutum ya yi akalla wa’adi guda cikakke a majalisa.
Wannan mataki ya hana Ugochinyere, wanda ke wa’adinsa na farko a majalisar, damar neman mukamin Jagoran ‘Yan Adawa a majalisar ta 10.
Ana sa ran wannan hukunci zai sauya yanayin takarar mukamin, inda hankali zai koma ga tsofaffin ‘yan majalisar adawa masu cikakkiyar gogewa da suka cancanci neman kujerar.
