Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Manyan Makarantu ta Kasa (JAMB) ta sanar da bude shafinta domin bai wa daliban da za su rubuta jarabawar Mop-Up UTME ta shekarar 2026 damar fitar da takardun bayanan jarabawarsu.
Mai magana da yawun JAMB, Fabian Benjamin, ya bayyana cewa daliban da abin ya shafa za su iya shiga shafin hukumar domin fitar da takardun da ke dauke da muhimman bayanai kafin ranar jarabawar da aka sanya a ranar 13 ga Yunin 2026.
Ya ce takardar na kunshe da bayanai kamar cibiyar da za a rubuta jarabawa, lokaci, rana da kuma sauran muhimman umarnin da za su taimaka wajen gudanar da jarabawar cikin sauki.
Benjamin ya bayyana cewa an shirya jarabawar Mop-Up ne domin daliban da suka rasa damar rubuta jarabawar UTME ta baya saboda matsalolin fasaha ko kuma wadanda ba a samu nasarar tantance bayanansu na biometric ba yayin jarabawar farko.
Ya bukaci daliban da suka cancanta da su gaggauta shiga shafin JAMB domin fitar da takardunsu tun da wuri, domin kaucewa matsalolin karshe.
Hukumar ta kuma shawarci daliban da su ziyarci cibiyoyin da aka ware musu kafin ranar jarabawar domin sanin wurin da kuma kaucewa jinkiri a ranar gudanar da ita.
JAMB ta jaddada cewa wannan ita ce dama ta karshe ga daliban da suka cancanta su rubuta jarabawar UTME ta 2026, tana mai gargadin cewa ba za a sake shirya wata jarabawar bayan wannan ba.
Saboda haka, hukumar ta bukaci daliban su yi shiri sosai tare da amfani da wannan damar yadda ya kamata.
