Boluwatife Fayose, ɗan tsohon gwamnan Jihar Ekiti, Ayodele Fayose, ya samu tikitin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) domin tsayawa takarar kujerar Majalisar Dokokin Jihar Ekiti a zaben 2027.
Sauran wadanda suka samu tikitin sun hada da Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Ekiti, Adeoye Aribasoye, mataimakin kakakin majalisar, Bolaji Olagbaju, da shugaban karamar hukumar Ekiti South-West, Richard Apolola.
Shugaban Kwamitin Zaben Fidda Gwanin APC na majalisar dokoki a jihar, Lateef Ibirogba, ne ya sanar da sakamakon bayan karbar rahotannin tattara kuri’u daga mazabu 26 na jihar.
Ibirogba ya bayyana cewa jam’iyyar ta yi amfani da tsari biyu wajen gudanar da zaben fidda gwani, inda aka tabbatar da ‘yan takara kai tsaye a mazabu 17, yayin da aka gudanar da zabe a sauran mazabu tara.
Ya ce wasu ‘yan takara sun samu tikiti ba tare da hamayya ba, yayin da wasu suka samu nasara bayan fafatawa da sauran masu neman takara a mazabunsu.
Daga cikin wadanda aka tabbatar kai tsaye akwai:
Ayorinde Ogunsakin (Ikole 1)
Olaoye Ogunsakin (Ekiti East 2)
Bose Olowookere (Efon)
Bolaji Olagbaju (Ado 2)
Adeoye Aribasoye (Ikole 2)
da sauran su.
A mazabun da aka gudanar da zabe kuwa, wadanda suka yi nasara sun hada da:
Ahmed Olutope (Ekiti East 1)
Monsurat Oladipupo (Ekiti West 1)
Richard Apolola (Ekiti South West 1)
Boluwatife Fayose (Irepodun-Ifelodun 2)
da wasu ‘yan takara da dama.
Nasarar Boluwatife Fayose na zuwa ne yayin da siyasar jihar Ekiti ke kara daukar zafi gabanin babban zaben 2027.
