Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma jigo a jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), Atiku Abubakar, ya bayyana gaban kwamitin tantance ‘yan takarar shugaban kasa na jam’iyyar a ranar Laraba, inda ya gabatar da takardunsa tare da bayyana shirinsa na farfado da tattalin arzikin Najeriya da kuma magance matsalar tsaro.
A cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan hulda da jama’a, Phrank Shaibu, ya fitar bayan tantancewar, Atiku ya ce zaman ba wai kawai domin tantance takardunsa ba ne, illa wata dama ce ta gabatar da hanyoyin ceto Najeriya daga matsin tattalin arziki, rashin aikin yi, tabarbarewar gwamnati da kuma matsalar tsaro da ta addabi al’umma.
Atiku ya bayyana cewa Najeriya ba za ta iya ci gaba da tafiya a wannan hali ba, inda iyalai ke fama da tsadar rayuwa, kasuwanci ke durkushewa saboda rashin tabbas a manufofin gwamnati, yayin da masu zuba jari ke rasa kwarin gwiwa.
Ya ce tsarin tattalin arzikin da ya gabatar ya ta’allaka ne kan samar da ayyukan yi, bunkasa bangaren masu zaman kansu, tsaftace harkokin kudade, da kuma dawo da martabar Najeriya a idon masu zuba jari.
Dangane da tsaro, Atiku ya nuna damuwa kan yawaitar kashe-kashe da garkuwa da mutane a sassan kasar nan, yana mai cewa babu wata gwamnati mai kishin jama’a da za ta zura ido ana kashe mutane ko sace su a gidajensu, gonakinsu da hanyoyi.
Ya ce shirinsa na tsaro zai mayar da hankali ne kan amfani da bayanan sirri, karfafa hadin gwiwar hukumomin tsaro, da bai wa jihohi damar taka rawa wajen tsaro, tare da nuna cikakken karfi wajen yakar masu aikata laifuka.
“At this defining moment in our national life, Nigeria does not need experiments. It needs tested leadership, clarity of vision, and the courage to make difficult but necessary decisions in the national interest,” in ji Atiku.
Ya kara da cewa yana da kudurin gina Najeriya mai tsaro, hadin kai da ci gaba, inda kowane dan kasa zai samu damar rayuwa cikin lumana da m0utunci.
