Mutane hudu sun rasa rayukansu bayan wata mota kirar Golf Wagon ta fada cikin madatsar ruwan Tomas da ke karamar hukumar Danbatta a jihar Kano.
Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta tabbatar da faruwar lamarin cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar, ACFO Saminu Abdullahi, ya fitar ranar Laraba.
A cewar sanarwar, hatsarin ya faru ne da misalin karfe 7:10 na yammacin ranar Talata bayan hukumar kashe gobara ta Danbatta ta samu kiran gaggawa daga wani mazaunin yankin mai suna Suleman.
An bayyana cewa motar, wacce ba a tantance lambar rajistarta ba, tana kan hanyarta daga Kano zuwa Roni a jihar Jigawa lokacin da ta fada cikin madatsar ruwan.
Sanarwar ta ce mutane 10 ne ke cikin motar lokacin da hatsarin ya faru.
“Jami’an kashe gobara daga ofishin Danbatta sun isa wurin cikin gaggawa kuma sun samu nasarar ceto dukkan wadanda hatsarin ya rutsa da su,” in ji sanarwar.
Hukumar ta bayyana cewa mutane hudu da aka ceto cikin halin suma daga baya likitoci suka tabbatar da mutuwarsu.
An gano sunayen biyu daga cikin mamatan da suka hada da Shamsiya Miko mai kimanin shekaru 35 da Fatima Danlami mai shekaru kusan 40, yayin da har yanzu ba a gano sunayen sauran biyun ba.
A cewar Abdullahi, an kai dukkan wadanda hatsarin ya shafa zuwa Asibitin Kwararru na Danbatta domin kula da lafiyarsu da sauran matakan da suka dace.
Binciken farko da hukumar ta gudanar ya nuna cewa fashewar taya ce ta haddasa hatsarin.
