Dan gwagwarmaya kuma tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, Omoyele Sowore, ya yi suka kan yadda ake tafiyar da batun sake takarar Shugaba Bola Ahmed Tinubu, inda ya nuna damuwa kan yadda wasu mutane ke cike masa fom ɗin takara.
Sowore ya yi wannan bayani ne bayan Ministan Ayyuka kuma tsohon Gwamnan Jihar Ebonyi, David Umahi, ya sanya hannu kan fom ɗin takarar shugaban ƙasa na Tinubu, wanda aka ruwaito kudinsa ya kai Naira miliyan 100.
A cikin wata sanarwa da mai taimaka wa Umahi kan harkokin yada labarai, Francis Nwaze, ya fitar, ya ce wannan mataki yana nuna goyon baya ga ci gaba da manufofin gwamnati da kuma tabbatar da nasarorin da aka samu.
Ya bayyana fom ɗin a matsayin “muhimmin mataki a tafiyar ci gaban Najeriya,” yana mai cewa yana nuna “ƙudirin ci gaba, kwanciyar hankali da kuma tabbatar da nasarorin gwamnatin da ke mulki.”
Umahi ya ce shugabancin Tinubu ya kawo sauye-sauye musamman a fannin gina hanyoyi da gyaran ababen more rayuwa, wanda ya ce yana da matuƙar muhimmanci ga ci gaban tattalin arzikin ƙasa.
Ya kuma ƙara da cewa shugaban ƙasa yana da damar kammala ayyukan da ake gudanarwa tare da zurfafa ci gaba a dukkan fannoni, inda ya yi kira ga ‘yan Najeriya su ci gaba da ba shi goyon baya.
A martaninsa ta shafin X, Sowore ya yi tambaya kan dalilin da yasa ake cike wa shugaban ƙasa fom ɗin zaɓe a madadinsa.
Ya kuma nuna damuwa ko hakan na nufin a nesanta shugaban ƙasa daga abin da ke cikin fom ɗin, musamman batun cancantarsa.
“Me yasa ake yawan cike wa Tinubu @officialABAT fom ɗin zaɓe alhali ba ya nan? Shin don ya nesanta kansa idan an rubuta masa abubuwan da ba su dace ba ko rashin cancanta?” in ji Sowore.
