Shugabar Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya (HoCSF), Misis Didi Esther Walson-Jack, ta yaba wa ma’aikatan gwamnatin tarayya bisa jajircewa, sadaukarwa da kuma ci gaba da yi wa kasa hidima.
A cikin sakonta na ranar Ma’aikata da ta fitar ranar Juma’a, Walson-Jack ta bayyana ma’aikatan gwamnati a matsayin ginshikin ci gaban kasa.
Ta ce dogon lokacin aiki da sadaukarwar da ma’aikata ke yi na tabbatar da tafiyar gwamnati da kuma isar da muhimman ayyuka ga ‘yan Najeriya.
“A kullum kuna tabbatar da cewa gwamnati tana aiki yadda ya kamata tare da samar da muhimman ayyuka ga al’umma. Ta fannin tsara manufofi, gudanarwa, ilimi, lafiya, tsaro, gine-gine da hulda da jama’a, kuna taka muhimmiyar rawa wajen ci gaban kasa,” in ji ta.
Ta kuma lura da yadda aikin gwamnati ke kara rungumar zamani ta hanyar kirkire-kirkire, amfani da fasahar zamani, inganta aiki, da ci gaba da koyon sabbin dabaru.
A cewarta, wannan sauyi na taimakawa wajen mayar da aikin gwamnati zuwa tsari mai inganci, saurin aiki, da mai mayar da hankali ga bukatun jama’a.
Walson-Jack ta kuma yabawa Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa abin da ta kira kulawa ta musamman ga jin dadin ma’aikata karkashin shirin Renewed Hope Agenda.
Ta bayyana wasu muhimman matakai da suka hada da:
Amincewa da tsarin tallafin ritaya ga ma’aikata
Aiwatar da tsarin diyya ga wadanda suka samu rauni yayin aiki
Karin alawus-alawus kamar Duty Tour Allowance, Estacode, da Book Allowance
Shirin bashin gidaje na Naira biliyan 10 ga ma’aikatan gwamnati
“Wadannan matakai hujja ne karara cewa gwamnati na daraja ma’aikata kuma tana kula da walwalarsu,” ta bayyana.
Sai dai ta gargadi ma’aikata da cewa lokaci ne na kara himma, kwarewa, gaskiya da samar da sakamako mai kyau.
“Ba lokacin sakaci ba ne. Lokaci ne na nuna kwazo da gaskiya wajen aiki,” in ji ta.
Ta bukaci ma’aikata da su kara habaka kwarewa, hada kai, rungumar sababbin dabaru da kuma ci gaba da aiki tukuru domin gina Najeriya mai karfi da wadata.
A karshe, ta gode wa dukkan ma’aikatan gwamnati bisa hidimarsu, tana mai cewa suna da matukar muhimmanci ga cigaban kasa.
