Gwamnan Jihar Anambra, Chukwuma Soludo, ya amince da nada sabbin shugabanni ga muhimman hukumomin lafiya a jihar, a wani mataki da gwamnati ta ce zai taimaka wajen inganta harkokin kiwon lafiya.
A cikin sabbin nade-naden, an nada Dr Ezeaka Uwaeme a matsayin Babban Sakatare na Hukumar Inshorar Lafiya ta jihar, yayin da aka nada Dr Obianuju Okoye a matsayin Babbar Sakatare ta Hukumar Kula da Lafiyar Matakin Farko. Haka kuma, an nada Dr Hillary Okeke a matsayin Daraktan Zartarwa na Hukumar Yaki da Cutar Kanjamau (AIDS) ta jihar.
Sanarwar nade-naden ta fito ne ta hannun Kakakin gwamnan, Christian Aburime, wanda ya bayyana cewa an zabi mutanen ne bisa kwarewa da gogewarsu a fannin kiwon lafiya.
A cewar sanarwar, Dr Uwaeme yana da fiye da shekaru 20 yana aiki a fannin likitanci da tiyata, tare da gogewa a bangaren asibiti da kuma gudanarwa.
Haka zalika, Dr Okoye tana da kwarewa a fannin lafiyar jama’a da kuma aikin likita, inda ta shafe sama da shekaru 20 tana aiki a bangaren kula da lafiya da gudanarwa.
Shi ma Dr Okeke kwararre ne a bangaren binciken cututtuka (epidemiology) da lafiyar duniya, tare da gogewa a bangaren koyarwa da aikin likita.
Gwamnatin jihar ta ce ana sa ran wadannan nade-nade za su taimaka wajen kara inganta tsarin kiwon lafiya, da kuma samar da ingantattun ayyuka ga al’ummar jihar.
