Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Yemi Osinbajo, ya bayyana farin cikinsa tare da yabawa kan kammala aikin gina gadar Angiama–Oporoma da ke Jihar Bayelsa, yana mai cewa aikin ya kasance mai matuƙar muhimmanci ta fuskar ci gaban tattalin arziki da haɗin kai tsakanin al’umma.
Ya ce gadar ta zama wata babbar nasara da ke cika alkawari, inda ya bayyana cewa an gina ta ne cikin gaskiya kuma tana nan a tsaye a yau a matsayin shaida ta ci gaba.
Osinbajo ya bayyana cewa wannan aiki na musamman ne ta fannoni da dama, domin ba kawai yana haɗa yankunan Agbura, Swali da sauran al’ummomi a Ƙaramar Hukumar Yenagoa ba, har ila yau yana buɗe hanyar Ogbia, inda ake da Jami’ar Tarayya ta Otuoke da kuma Oloibiri—wurin da aka fara gano man fetur a Najeriya.
Ya ce wannan yana ɗauke da muhimmiyar ma’ana ta tarihi da tattalin arziki.
Haka kuma, gadar tana haɗa manyan cibiyoyin gwamnati da suka haɗa da ginin NCDMB Towers, Federal Secretariat, da kuma hedikwatar CBN a Jihar Bayelsa.
“Wannan hanya tana da matuƙar muhimmanci. Ina farin ciki da kuma alfahari da kasancewa wanda zai kaddamar da wannan gagarumin aiki,” in ji shi.
A nasa jawabin, Gwamnan Jihar Bayelsa, Douye Diri, ya bayyana cewa tun a shekarar 2022 ya jajirce wajen ganin an fara aikin, inda ya gayyaci Osinbajo domin kaddamar da shi.
Ya ce aikin ya samar da ayyukan yi ga daruruwan matasa daga yankunan da ke kusa, yayin da ake gudanar da aikin gini.
Diri ya ƙara da cewa sabon hanyar ta buɗe damar tattalin arziki, tare da sauƙaƙa sufuri da isa ga ƙarin al’ummomi masu rayuwa a yankunan koguna.
Ya kuma tuna cewa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taɓa ziyarar tarihi zuwa Bayelsa domin kaddamar da wani ɓangare na aikin, wanda ya nuna muhimmancin aikin ga jihar da ƙasa baki ɗaya.
A ƙarshe, gwamnan ya taya al’ummar Bayelsa murna bisa wannan gagarumar nasara da ake ganin za ta ƙara inganta ci gaban jihar.
