Tsohon ɗan wasan ƙwallon ƙafa na Najeriya, John Obi Mikel, ya caccaki kungiyar FC Barcelona bayan fitar su daga gasar UEFA Champions League, yana mai cewa rashin “killer instinct” ne ya jawo musu rashin nasara, ba laifin alkali ba.
Barcelona ta yi rashin nasara da jimillar kwallaye 3–2 a hannun Atlético Madrid, lamarin da ya jawo cece-kuce daga ‘yan wasa da jami’an kulob din, inda suka zargi alkali da rashin adalci a wasan.
Sai dai Mikel Obi, wanda ya yi hira da jaridar Mundo Deportivo, ya yi magana mai zafi inda ya ce Barcelona ta yi yawa wajen mallakar kwallo amma ta kasa amfani da damar da ta samu.
“FC Barcelona fans ba za su ji dadin abin da zan fada ba, amma gaskiya ne,” in ji Mikel.
“Kun mallaki kwallo amma kun kasa yin amfani da ita. Sannan idan gaskiya ta bayyana sai ku fara cewa an cuce ku.”
Ya kara da cewa abin da ya faru ba “robbery” ba ne, illa kawai rashin kwarewa wajen kammala damar da suka samu a wasa.
“Wannan ba sata ba ce. Kun fallasa kanku ne da rashin killer instinct. Atlético Madrid sun nuna karfi da hali a lokacin da aka fi bukata.”
Mikel ya kuma yi ishara da yadda wasu ‘yan wasa suka kasa daukar nauyi a wasan karshe, yana mai cewa Barcelona ba ta nuna karfin dawowa daga baya ba duk da damar da ta samu a wasanni biyu.
Rahotanni sun kuma danganta tasirin dan wasan Ademola Lookman a wasu muhimman lokuta na wasan, inda ya taka rawar gani wajen tabbatar da nasara ga abokan hamayya.
Mikel ya kammala da cewa zargin alkali ba zai canza sakamakon wasa ba, yana mai cewa dole Barcelona ta kalli kanta idan tana son dawowa da karfi a nan gaba.
