Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da wani kwamiti na fasaha domin nazarin shirin gina layin dogo mai sauri da kuma samar da wutar lantarki ta gas mai tsawon kilomita 4,000 a fadin Nigeria.
Shirin, wanda zai gudana ƙarƙashin kulawar Infrastructure Concession Regulatory Commission, zai ratsa dukkan jihohi 36 na ƙasar tare da haɗa muhimman hanyoyin tattalin arziki.
An bayyana cewa za a aiwatar da aikin ne ta hanyar haɗin gwiwar gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu (PPP).
Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume, ne ya ƙaddamar da kwamitin a ranar Alhamis a Abuja, inda ya ce shirin zai haɗa manyan birane kamar Lagos, Abuja, Kaduna, Kano da kuma Port Harcourt.
Akume ya ƙara da cewa an gabatar da shirin ne daga wata haɗakar kamfanoni da DE-SADEL Consortium Nigeria Ltd. ke jagoranta, tare da haɗin gwiwar China Lansay Petroleum Investment Holdings Ltd., kuma ana hasashen kudin aikin zai kai dala biliyan 200.
A cewarsa, an tsara aikin ne a matakai daban-daban, wanda ya haɗa da bunƙasa gas, samar da wutar lantarki da jigilar ta, tare da gina layin dogo mai sauri a fadin ƙasar.
Ana sa ran wannan babban aiki zai taimaka wajen inganta sufuri, ƙarfafa tattalin arziki da kuma samar da wutar lantarki mai ɗorewa ga ‘yan ƙasa.
