Uwargidan shugaban kasa, Oluremi Tinubu, ta bukaci ‘yan Najeriya da su yi amfani da lokacin bikin Easter wajen nuna kauna da taimakawa marasa galihu a cikin al’umma.
Ta bayyana hakan ne a ranar Juma’a a Abuja cikin sakon ta na Easter mai taken “Fatan Albarka cikin tashin Almasihu”, yayin da Kiristoci a duniya ke tunawa da mutuwa da tashin Jesus Christ daga matattu.
Uwargidan shugaban kasar ta jaddada cewa Easter wata dama ce da ke tunatar da mutane muhimmancin kauna da sadaukarwar da Yesu Almasihu ya nuna yayin rayuwarsa a duniya.
Ta ce:
“Easter yana tunatar da mu ikon kauna da sadaukarwa, da kuma bege da tashin Almasihu ke kawo wa bil’adama baki daya.
Ta kuma bukaci ‘yan Najeriya da su tuna da marasa karfi da masu bukata yayin shagulgulan, tare da nuna musu tausayi da taimako.
A cewarta:
“Yayin da muke bikin Easter tare da iyalai da abokai, mu tuna da wadanda ke cikin bukata, mu taimaka musu kuma mu nuna musu kauna.”
A karshe, ta yi addu’ar cewa ruhin Easter ya zaburar da al’umma wajen taimakon juna, inganta zaman lafiya, da kuma gina kasa mai ci gaba da wadata ga kowa da kowa
