Shugaban kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars, kuma kyaftin din tawagar Super Eagles na Najeriya, Ahmed Musa (MON, OON), ya sha alwashin gyara kungiyar da dawo mata da martabarta a matsayin daya daga cikin manyan kungiyoyin kwallon kafa a nahiyar Afrika.
A wata taron sanin makamar aiki da aka gudanar ranar Litinin tare da Shugaban Kungiyar, Alhaji Ali Muhammad Umar, da sauran mambobin kwamitin gudanarwa, Ahmed Musa ya nuna cikakken niyyarsa ta inganta kungiyar da kuma gina sabuwar Kano Pillars mai cike da tarihi da nasarori.
A cewar Sashen Watsa Labarai da Sadarwa na Kano Pillars FC, Ahmed Musa — wanda ya buga wasa a manyan ƙungiyoyi kamar Leicester City da CSKA Moscow — ya ce lokaci ya yi da za a yi aiki tukuru domin samar da martabar duniya ga Kano Pillars, wacce ta lashe gasar Najeriya sau hudu.
Ya bayyana cewa yana shirye ya hade gwiwa da dukkan masu ruwa da tsaki, a cikin gida da wajen ƙasar, domin cimma wannan buri. Musa ya ce gwanintarsa a Turai da fahimtarsa da kwallon kafa ta gida zai ba shi damar kawo canji mai amfani ga kungiyar.
> “Kano Pillars tamu ce, kuma na daya daga cikin mafi nasara a Najeriya, amma a ‘yan shekarun nan lamarin ya sauya. Ina tabbatar muku da cewa, da goyon bayanku da na kwamitin gudanarwa, zan yi iya kokarina wajen dawo da Pillars zuwa inda ta dace – ba kawai a Afrika ba, har ma a duniya,” inji Ahmed Musa.
Ya jaddada cewa nasarar kungiyar zai samu ne idan aka hada kai gaba daya, tare da tsara aiki cikin dabaru da sadaukarwa daga kowa: shugabanci, ‘yan wasa, magoya baya, da masu daukar nauyi.
A tuna cewa, gwamnatin Jihar Kano karkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf ce ta nada Ahmed Musa a matsayin General Manager na Kano Pillars domin dawo da martabar kungiyar ta hanyar bin tsarin gudanarwa na zamani.
Tare da Musa a kan gaba, ana sa ran Kano Pillars za ta shiga sabon zamani na girma, kwarewa da nagarta, wanda zai zamo abin alfahari ba kawai ga Kano ba – har da dukkan magoya baya a Najeriya da wajen ƙasa.
