Tsofaffin jami’an rundunar ƴan sandan Najeriya sun fara gudanar da zanga-zangar lumana a Abuja da
wasu jihohi, domin nuna rashin jin daɗinsu kan tsarin fansho da ake amfani da shi a yanzu.
Sakamakon hakane, Sufeto Janar na ƴansandan Najeriya, Kayode Egbetokun, ya umarci dukkan kwamishinonin ƴansanda a faɗin ƙasar da babban birnin tarayya Abuja (FCT), da su samar da tsaro yayin wannan zanga-zangar.
Kakakin rundunar ƴansandan Najeriya, ACP Olumuyiwa Adejobi, ya bayyana hakan a wata sanarwa, inda ya ce an samu yunkurin yaɗa bayanan ƙarya domin ɓata sunan gwamnati da na rundunar ƴansandan.
Ya ce kiraye-kirayen da tsofaffin jami’an ke yi na fita daga tsarin fansho da ake amfani da shi a yanzu ba sabon abu ba ne, kuma waɗanda suka riƙe muƙamin sufeto Janar a baya sun goyi bayan hakan, amma wasu matsaloli na doka da na kuɗi sun hana ci gaban hakan.
Add A Comment