A wata babbar masifa da ta auku a Mokwa, jihar Niger, an tabbatar da mutuwar mutane 206 sakamakon ambaliya mai tsanani.
Ruwan sama mai ƙarfi da ya kwashe gidaje, gona da abinci ya bar dubban mutane ba matsuguni. Hukumar NEMA ta fara rabon agaji amma har yanzu matsalar ta yi muni sosai.
> 🔹 Hukumar Lafiya da ta Jin Kai ta ƙasa ta ce ana bukatar taimako na gaggawa domin kare lafiyar jama’a da rage yaduwar cututtuka.
Gwamnatin jihar ta bayyana alhini tare da kafa kwamitin bincike kan musabbabin ambaliyar, da yadda za a magance irin wannan a gaba.
🟦 Asrah 24 TV – Gaskiyar Zance
