Close Menu
  • Home
  • News
    • National
    • International
  • Asrah 24 TV
  • Education
  • Health
  • Podcast
  • Politics
  • Sports
  • More
    • Agriculture
    • Business
    • Climate Changes
    • Culture
    • Environment
    • Entertainment
    • Opinion
    • Religious
    • Security
    • Videos
Facebook X (Twitter) YouTube WhatsApp Telegram
Facebook X (Twitter) WhatsApp Telegram
ASRAH 24 MEDIA
Subscribe
  • Home
  • News
    1. National
    2. International
    3. View All

    Najeriya Ta Kai Dala $18.4 Biliyan a Cinikayyar Cikin Afirka a 2024

    June 28, 2025

    Afreximbank Ta Ba Najeriya Tallafin $50 Biliyan Don Manyan Ayyuka

    June 28, 2025

    Mutane 28 sun mutu sakamakon gudun wuce sa’a a jihar Ondo- FRSC

    February 2, 2025

    Najeriya Ta Fuskanci Limit na Visa zuwa Amurka – 3 Mako Kaɗai!

    July 9, 2025

    Gwamnatin Tarayya Tare da Faransa Za Su Inganta ICT a Jami’o’in Najeriya da Tallafin Naira Biliyan 38

    July 4, 2025

    Zafin Rana Mai Tsanani Ya Ɓarke a Turai: Matsalar Heat Dome

    June 30, 2025

    Najeriya Ta Samu Jarin Waje Har Dala Biliyan 2.5 Daga Masarautar Saudiyya

    June 29, 2025

    Jihohi sun raba Naira biliyan 22.9 a matsayin kudin gyaran muhalli

    September 1, 2025

    Gwamna Bago Ya Rusa Majalisar Ministocinsa a Neja

    September 1, 2025

    Atiku Ya Bukaci Jam’iyyun Adawa Su Ƙi Karɓar Sakamakon Zaɓen Rivers

    September 1, 2025

    Tinubu ya na adalci ga kowanne yanki na ƙasar nan – Ministan Yaɗa Labarai

    September 1, 2025
  • Asrah 24 TV
  • Education

    Ƴar Najeriya ta lashe gasar iya Turanci ta duniya a London

    August 5, 2025

    Yan Kano 3 Sun Yi Nasarar Lashe Gasar Nazarin Tarihin Shehu Usman Dan Fodio A Najeriya Wani gagarumin farin ciki ya bayyana a jihar Kano bayan dalibai uku daga makarantar Rumfa College suka lashe gasar kasa ta nazarin tarihin Shehu Usman Dan Fodio da aka gudanar a Abuja. Gasar wadda ta haɗa jihohi 17 na Arewa, ta nuna hazakar matasan Kano inda suka samu kashi 96% na maki gabaɗaya. > “Mun yi nasara ne saboda muna jin dadin tarihinmu. Shehu Dan Fodio ya ba mu abin alfahari,” in ji ɗaya daga cikin daliban da suka yi nasara. Gwamnatin Kano ta sha alwashin ba su kyautar karatu da tallafi na musam

    August 1, 2025

    NSUBEB ta Bukaci ‘Yan NYSC su Auri Mutane a Jihar Nasarawa

    July 10, 2025

    Ɗalibar Najeriya Ta Lashe Gwarzon Daliba A Oxford

    June 29, 2025

    Gwamnatin Kano ta baiwa dalibai hutun bikin Sallah Babba

    June 1, 2025
  • Health

    WHO Ta Tabbatar Da Sabon Magani Mai Karfi Akan Ciwon Sikila da Sankarau

    June 29, 2025

    Gwamnatin Najeriya za ta fara bada agajin gaggawa kyauta ga marasa Lafiya a Kano

    May 17, 2025

    Cutar Zazzabin Lassa Ta Hallaka Mutane 80 a Najeriya Cikin Mako Daya

    February 25, 2025

    Mutane 28 sun mutu sakamakon gudun wuce sa’a a jihar Ondo- FRSC

    February 2, 2025
  • Podcast
  • Politics

    Gwamnatin Kano Ta Kaddamar da Yakin Kakkabe Malaria

    July 30, 2025

    Keyamo ya Caccaki Atiku kan Sauya Sheka a Lokacin Makokin Rasuwar Buhari

    July 17, 2025

    Gwamna Abba Yusuf Ya Nada Sabon Chief of Staff da DG Special Services

    July 13, 2025

    Gwamnatin Kano Na Neman Ƙara Jiha Guda da Kananan Hukumomi 26

    July 13, 2025

    Yabo Gagarumi Ga Gwamna Abba Yusuf Kan Tsare-Tsaren Hajjin Bana

    July 13, 2025
  • Sports

    Ahmed Musa Ya Yi Alkawarin Dawo da Kano Pillars Zuwa Matsayinta na Gaba da Gaba a Afrika

    July 10, 2025

    Tsohon Goalkeeper Peter Rufai Ya Rasu

    July 4, 2025

    Najeriya ta doke kasar Egyp da ci 4-1: U-20 AFCON

    May 19, 2025

    FIFA ta amince da kasashe 48 su halarci gasar cin kofin Duniya ta Mata a shekarar 2031

    May 10, 2025

    Flying Eagles ta doke kasar Egyp a shirye-shiryen fara tun karar gasar AFCON

    April 23, 2025
  • More
    • Agriculture
    • Business
    • Climate Changes
    • Culture
    • Environment
    • Entertainment
    • Opinion
    • Religious
    • Security
    • Videos
ASRAH 24 MEDIA
Home » Gwamnatin Najeriya za ta fara bada agajin gaggawa kyauta ga marasa Lafiya a Kano
Health

Gwamnatin Najeriya za ta fara bada agajin gaggawa kyauta ga marasa Lafiya a Kano

Asrah24 MediaBy Asrah24 MediaMay 17, 20253 Mins Read
Facebook Twitter WhatsApp
polish save

Gwamnatin tarayya ta kaddamar da wani sabon shiri na bayar da agajin gaggawa ga marasa lafiya a jihar Kano, wanda ya fara da amincewar Asibitin Kashi na Dala, dake Kano, karkashin hukumar bada agajin gaggawa ta kasa (NEMSAS).

Da yake jawabi yayin bikin kaddamar da shirin ranar Juma’a a asibitin, babban daraktan kula da lafiya, Dakta Nurudeen Isa, ya ce shirin ya nuna wani babban ci gaba a fannin kiwon lafiya ga gwamnati mai ci, da nufin bayar da kulawa ga marasa galihu.

“A yau, mun gayyace ku da ku baje kolin daya daga cikin muhimman abubuwan kiwon lafiya na wannan gwamnati na bayar da kulawar gaggawa ga duk marasa lafiya da aka kawo daga kowane yanki na wannan jiha zuwa wannan asibiti, inda zai su sami kulawar lafiya kyauta cikin sa’o’i 48 na farko,” in ji Dakta Isa.

Ya bayyana cewa, NEMSAS, wata kafa da gwamnatin tarayya ta samar da kudaden da ake samu kai tsaye daga asusun tarayya, an tsara shi ne domin tabbatar da cewa dukkan ‘yan Nijeriya, musamman ma marasa galihu, sun sami damar samun kulawar ceton rai a cikin gaggawa.

SolaceBase ta ruwaito cewa shirin ya kunshi majinyata da suka hadu da hadurran ababen hawa, da gaugawar haihuwa, saran maciji, harbin bindiga, da sauran munanan yanayi.

Wannan shi ne wuri na farko a jihar Kano da aka amince da shi a karkashin wannan shirin. Sauran, da suka hada da asibitocin gwamnatin jihar, nan ba da jimawa ba za a yi musu rajista,” ya kara da cewa, shirin zai iya ceton rayuka da kuma hana afkuwar rikice-rikice a lokutan gaggawa.

Shima da yake jawabi a wajen taron, Dakta Emuren Doubra, shugaban aiyuka na NEMSAS, wanda ya wakilci Dr. Said Ahmed Dumbulwa, Darakta/ Manajan Shirye-shiryen NEMSAS daga Ma’aikatar Lafiya ta tarayya, ya tabbatar da dorewar shirin, wanda ke samun goyon bayan tallafin da doka ta tanada daga asusun kula da lafiya na kasa da ke tushen tsarin kiwon lafiya na kasa.

“Daga wannan asusun, an ware kashi 5% na musamman don kula da lafiyar gaggawa. Muna hada kai da masu zaman kansu da kuma cibiyoyin kiwon lafiya na jama’a don tabbatar da cewa ba a bar ‘yan Najeriya matalauta da marasa galihu su dauki nauyin kulawar gaggawa,” in ji Doubra.

A wani bangare na aiwatar da shirin, shirin ya hada da tawagar motocin daukar marasa lafiya sanye da kayan aikin jinya da ma’aikata, tare da hadin gwiwar hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC), domin jigilar wadanda hadarin ya rutsa da su da sauran majinyatan gaggawa daga kowane wuri a cikin jihar Kano zuwa asibiti.

Wadannan motocin daukar marasa lafiya ba na sufuri ba ne kawai. Suna ba da kulawar gaggawa tun daga wurin da lamarin ya faru kuma suna sanar da asibitin tukuna don a yi shirye-shiryen karbar mara lafiyar,” Dr. Dumbulwa ya bayyana.

Wani majinyaci da ya ci gajiyar shirin, Aliyu Abdul, ya bayyana cewa a baya an gaya masa a asibitocin Enugu da Legas cewa za a yanke kafar sa sakamakon wani mummunan hatsari da ya faru.

“Lokacin da na yi hatsari, an gaya mini cewa za a yanke kafata, amma da na zo nan, na sami ingantaccen magani.

“Yanzu na murmure – kun ga ina tsaye,” in ji shi, yana nuna godiya ga sa’o’i 48 na jinya kyauta.

Ana sa ran shirin zai fadada zuwa wasu asibitoci a fadin jihar Kano tare da zama abin koyi wajen bayar da agajin gaggawa a fadin kasar.

Share. Facebook Twitter Telegram WhatsApp
Previous ArticleMajalisar Dokokin jihar Kano tace Hukumar KAROTA batada Hurumun Kama masu karya dokokin titi a jihar Kano
Next Article Zamu ci gaba da karya farashin kayan abinci a Najeriya: BUA

Related Posts

WHO Ta Tabbatar Da Sabon Magani Mai Karfi Akan Ciwon Sikila da Sankarau

June 29, 2025

Cutar Zazzabin Lassa Ta Hallaka Mutane 80 a Najeriya Cikin Mako Daya

February 25, 2025

Mutane 28 sun mutu sakamakon gudun wuce sa’a a jihar Ondo- FRSC

February 2, 2025
Add A Comment
Leave A Reply Cancel Reply

Latest Posts

Jihohi sun raba Naira biliyan 22.9 a matsayin kudin gyaran muhalli

September 1, 2025

Gwamna Bago Ya Rusa Majalisar Ministocinsa a Neja

September 1, 2025

Atiku Ya Bukaci Jam’iyyun Adawa Su Ƙi Karɓar Sakamakon Zaɓen Rivers

September 1, 2025

Tinubu ya na adalci ga kowanne yanki na ƙasar nan – Ministan Yaɗa Labarai

September 1, 2025

An Kama Fitaccen Ɗan Daba da Abokinsa a Kano Saboda Bidiyon Nuna Makamai da Yaɗu Sosai

August 28, 2025
Connect with us
  • Facebook
  • Twitter
  • YouTube
  • WhatsApp
  • Instagram
  • TikTok
Top Posts
Advertisement
© 2026 ASRAH 24 MEDIA. Developed by ENGRMKS & CO..
  • Home
  • About Us
  • Contact Us
  • Privacy Policy

Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.