Gwamnan Jihar Rivers, Siminalayi Fubara, ya rubuta wasika ga shugaban majalisar dokokin jihar, Martin Amaewhule, yana neman damar sake gabatar da kasafin kudin shekarar 2025.
A cikin wasikar da aka rubuta ranar 13 ga Maris, Fubara ya bukaci majalisar ta ba shi damar bayyana kasafin kudin a duk lokacin da ya dace da su.
Gwamnan ya bayyana cewa jami’an tsaro sun hana shi shiga zauren majalisar a ranar Laraba da ta gabata, duk da cewa ya sanar da shugabanta shirin sa na gabatar da kasafin. Ya ce matakin da ya dauka yana da alaka da bin umarnin Kotun Koli, wadda ta bukaci sake gabatar da kasafin kudin ga majalisar.
